Nnamdi Kanu zai fuskanci tuhuma
September 26, 2025
Kotun karkashin mai shari'a James Omotosho ta yi fatali da bukatar jagoran 'yan awaren na IPOB Nnamdi Kanu ta a sake shi yana mai cewa masu gabatar da kara sun gabatar da wadatattun shaidu da ke nuna tilas ya amsa laifukan cin-amanar kassa da ta'addanci, tare da dage sauraron shari'ar zuwa ranar takwas ga watan Oktbar da ke tafe.
Yiwuwar fuskantar hukuncin kisa
An dai fara kama Kanu dan Najeriya da ke da fasfo din kasar Birtaniya kana jagoran kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta IPOB da gwamnati ta haramta, a shekara ta 2015 a Najeriya. Sai dai ya tsere bayan da aka bayar da belinsa a shekara ta 2017, inda aka sake kama shi a kasar Kenya a shekara ta 2021 kafin a tuhume shi da laifuka da dama da ke da alaka da ta'addanci da za su iya sawa ya fuskanci hukuncin kisa.
Wanne yanayi lafiyar Kanu ke ciki?
Kotun ta kuma bukaci a samar da likitoci takwas da za su duba lafiyarsa, sai dai mai gabatar da kara na gwamnati Adegboyega Awomolo ya nuna adawarsa da matakin yana mai cewa amincewar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriyar wato DSS ka iya janyo barazanar tsaro kana hukumar ta DSS ta yi biyayya ga dukkanin umurnin kotun kan daukar matakan jin dadinsa.