Najeriya: Coronavirus ta janyo tsaiko a aikin layin dogo
March 6, 2020![Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna](https://static.dw.com/image/19428430_800.webp)
Talla
Ministan ya kara da cewar ma'aikatan da suka tafi gida hutun sabuwar shekararsu, sun makale ne bayan da Coronavirus tai kamari, aiki da ya kamata a kamala shi a watan Mayun da ke tafe bisa dukkan alamu hakan ba zai yiwu ba.
Ya zuwa yanzu dai wannan annobar Coronavirus ta janyo asara mai yawa a fani daban-daban na alamuran yau da kullum. Yanzu mutum dubu dari ne suka kamu da cutar a fadin duniya, yayin da sama da mutum dubu uku suka mutu a sanadiyarta.
Kasashe hudu dake a Kudu da sahara suka sami bullar cutar sai dai ba tai kamari ba duk kuwa da mu'amalar da ke tsakanin China da kasashen.