1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da rikicin Afirka a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar MAB
February 5, 2021

Jaridar Die Tageszeitung ta rubuta sharhi mai taken" Shell zai biya kudin diyya saboda gurbata muhalli" a Najeriya bayan hukunci da kotu ta yanke wa kamafanin mai na Shell, hukuncin da ake wa kallon ya na da illoli.

Shell I Tankstelle I Energie
Hoto: Schoening/Bildagentur-online/picture-alliance

Wata kotu da ke da matsugunni a birnin The Hague na kasar Netherlands ta yanke wa kamafanin albarkatun mai na Shell hukuncin biyan kudaden diyya ga wasu manoman yankin Niger Delta da ke kudancin Nageriya, hukuncin da ake wa kallon ya na da illoli.

Jaridar Die Tageszeitung ta ce an samu katafaren kamfanin na Royal Dutch Shell da laifin gurbata muhalli a Najeriya. A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai aka yanke wannan hukuncin bayan daukaka kara da manoman suka yi bayan hukuncin farko da ba su amince da shi ba. Kamfanin a daya bangaren ya dora alhakin lalata muhallin kan masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta. Hukuncin kotun na birnin The Hague na nuni da cewar kauyuka biyu ne za a biya mukudan kudade biyo bayan bata musu filayen noma, duk da cewar ba a sanar da yawan kudin da za a  biya ba. 

Manoman yankin Niger Delta sun yi nasarar a kan ShellHoto: AP

Wata kungiyar fafukar kare muhalli da wasu manoma hudu ne dai suka shigar da karar kamfanin na Shell a gaban kotu a shekara ta 2008, saboda gurbata filayensu da mai da kamfanin ya yi. Duk da cewar kotun kai tsaye ba ta sami kamfanin da laifin ba, ta ce hakkin kula da al'umma da abubuwan da ke gudana a kewayensu ya rataya a wuyan shell. Hukuncin dai ya samu martanin farin cikin daga bangaren masu shigar da karar.

 

Allurar corona ta zama tamkar zinare a Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ta fara samun allurar rigakafin cutar corona. Sai dai ba za ta wadata al'umma ba, da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta bude labarin da ta rubuta game da halin da ake ciki na ta'azzarar cutar corona a wannan kasa. A cewar jaridar matakan da aka dauka a yayin ake sauke damin alluran tamkar gwala gwalai ne da lu'u lu'u suka iso babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Johannesburg.

Allurar rigakafin corona ya isa Afirka ta KuduHoto: via REUTERS

An dai killace fillin jirgin, kana jami'an soji dauke da bindigogi na ta sintiri. Kai tsaye gidan talabijin na kasa ya nuna saukar jirgin Emirates da ke dauke da zangon farko na allurar coronar. Shugaba Cyril Ramaphosa da mataimakinsa tare da ministan lafiya na Afirka ta Kudun ne suka karbi allurar rigafin guda dubu 500, wanda ke zama irin sa na farko zuwa wata kasar Afirka da ke yankin kudu da Sahara, allurai rabin miliyan wa mutane sama da biliyan guda. 

A yayin da ake tsara yadda za a gudanar da rigakafin da wadanda ya dace a basu, Afrika ta Kudun na jiran zango na biyu na allurar coronar miliyan guda daga Indiya. Mutane da dama sun shiga shirin bincike na ingancin alluran kamfanoni uku watau Johnson & Johnson da AstraZeneca da Novavax. Sai dai hakan baya nuna cewar, suna cikin masu cin gajiyarsa. 

 

Mazauna yankin Tigray sun shiga mawuyacin hali

Daga batun corona sai kuma halin tagayyara da 'yunwa da al'ummar yankin Tigray na kasar Habasha suka tsinci kansu a ciki, wanda ke zama mafi munin irinsa da kasar ba ta gani ba tun a shekarun 1980 a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung.Tsawon watanni uku kenan ake gwabza fada a wannan yanki, kuma a kullum yanayin rayuwa sai kara kazancewa yake. Kwararru sun yi nuni da cewar, Ethiopiyar ba ta taba ganin irin wannan mawuyacin hali ba tun bayan 'yunwa sakamakon farin da ya kashe sama da mutane miliyan guda a shekarun 1980.

'Yan gudun hijiaran Tigray na neman abinci a SudanHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Halin da Tigray ke ciki baya misaltuwa. Babu hanyar sadarwa ta Intanet, an hana 'yan jarida zuwa yankin tun bayan barkewar yaki. Abun da kawai aka sani shi ne, mutane miliyan biyu sun rasa matsugunnensu, a yayin da wajen dubu 60 suka tsere zuwa Sudan da ke makwabtaka, bayan dubban da suka rasa rayukansu.