1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun na Jamus sun yankunan rikici na Afirka.

Usman Shehu Usman
September 3, 2021

Yafe wa tubabbun mayakan Boko Haram da mahukuntan Najeriya ke yi, da rikicin yankin Sahel na Afirka da shirin zaben São Tomé da Príncipe, sun dauki hankalin jaridun na Jamus.

Presseschau Deutsche Zeitungen
Hoto: DW

Za mu fara sharhunan jaridun Jamus kan Afirka ne, bisa labarin mayar da tubabbun mayakan Boko Haram jihar Borno izuwa garuruwansu na asali. Jaridar die Tageszeitung ce ta rubuta labarin. Jaridar ta ce duk hatsarin da wasu ke cewa na tattare da sake mayarda irin wadannan mayaka kauyukan, amma kuma yin haka shi ne mafi alheri. Gwamnatin Jihar Borno ta kuduri anniyar kimanin mayaka 3000 gidajensu, domin a yanzu sun tuba kuma lokaci ne na sake bada dama su saje da sauran al'umma. Jaridar ta ce a karshen makon shugabannin addinai da sarakunan gargajiya hadi da kungiyoyin farar hula ne suka taru don bikin na sake mayar da wadannan mutane garuruwansu. 

Jaridar die Tageszeitung ta kuma yi waiwai izuwa wasu yankunan da ake fama da yaki da ta'addanci, wato kasashen yankin Sahel. Ta fara labarin a Sahel cewa, karfin soja kadai bai wadatar ba a yaki da ta'addanci. Ta bada misali da Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso da Mali. Jaridar ta ce kama daga tsakiyan watan jiya mutane samam da 80 suka mutu sakamakon hare-haren ta‘addanci a kasar Burkina Faso.

Birnin Gorgadji shi ne yankin baya-bayannan da aka kai wa harin ta'addanci. Yankin dai nai yaka ne da Nijar da kuma kasar Mali. Shugaban kasar ya sanar da ranakun makoki, amma kuma har sau nawa za a yi irin wadannan ranakun makoki, domin kuwa da an kai hari yau, kafin a kammala sadakar uku sai ka ji an sake kai hari ta wani bangaren. Wadannan hare-hare na faruwa ne duk irin damar yaki da kasashen suka yi, ga kuma dumbin dakarun kasashen waje da ke ciki su ma da sunan yaki da ta'addanci amma kuma bai hana aukuwar hare-haren ba, don haka wata kila karfin bindiga ba shi ne kadai maganin hare-haren ta'addanci ba.

Kasar Afirka ta Kudu na bukatar maganin shaku da jama'a ke yi bawai alluran riga kafi kawai ba. Jaridar Frankfurter Algermeine Zeitung ta yi wannan labari.Jaridar ta ce bayaga karancin alluaran riga kafi, amma fa akwai matukar bukatar wayar da kan jutane, domin kyamar da ake yi wa alluran yanzu yanan da matukar tasiri tsakanin al'umma. Don haka ta bada misali cewa, akwai wasu yankuna da za ka je ka samu magungunan da aka sayo suna cike a wuraren adanarsu amma kuma jama'a suna ci gaba da dari-darin yin allurar. Misali wata ‘yar shekaru 23 da jaridar ta yi hira da ita kan riga kafin corona. Cewa ta yi a wannan kasar fa gwamnati ba ta bayar da abu kyauta, kuma ya aka yi yanzu corona ake bada alluranta kyauta, wannan cewar yarinyar akwai bukatar yin nazari. Kuma ba wai ga wannan da aka yi hira da ita kawai, lamarin haka yake ga mutane da yawa.

Sai Jaridar Neue Zürcher Zeitung, wace ta duba zaben kasar São Tomé da Príncipe da zai gudana a wannan karshen mako. Jaridar ta ce wannan mitsitsiyar kasa ta kasance wace aka fi samun dorewar demokradiyya a Afirka. Tun shekara 1990 ake mulkin demokradiyya, kuma a na samun sauyi daga wannan jam'iyya zuwa wancan, kasar wace tsibirai biyu suka hadu suka zama kasa daya, suna gabar tekun Gini. Inda suka samu 'yancin kai daga kasar Portugal a shekara ta 1975. São Tomé da Príncipe ta dogara ne da noman koko da kofi haka kuma tsbirin na cikin wadanda ke samun baki masu yawon shakatawa. Za dai a gudanar da zaben kasar ne a wannan Lahadi, kuma alamu na nuna babar jam'iyar adawa na iya lashe zaben.