1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakon ceto yaran makaranta da aka sace a Katsina

Uwais Abubakar Idris MNA
December 14, 2020

A lokacin da mahukuntan Najeriya ke ba da tabbacin za su gano daruruwan daliban da aka sace daga wata sakandare a garin Kankara a jihar Katsina, ana ci gaba da mayar da martani da ma yin tir da abin da ya faru.

Nigeria Katsina | Kankara | Angriff auf Schule
Hoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

Duk da tabbaci na fatar baka da ma jibge jami'an tsaro don ceto yaran da aka sace daga makarantar sakandare ta garin Kankara a jihar Katsina, kalamai daga Majalisar Dinkin Duniya ya zuwa asusun kula da lafiyar yara na majalisar da ma sauran kungiyoyi na kasa da kasa batun Allah wadai ne da ma bukatar hanzarta ceto daliban makarantar sakandaren ta garin Kankara da har zuwa yanzu babu zahiri na adadin yawansu. Ana ja in ja a tsakanin fadar gwamnatin Najeriyar da gwamnan jihar Katsina a kan batun da ke  kara nuna zahirin abubuwan da ke faruwa. Dr Yahuza Getso masani ne a fannin tsaro a Najeriyar ya bayyana illoli na zahiri ga abin da ya faru da ma matakan da gwamnati ta dauka na rufe ilahirin makarantun a jihar. Karin bayani: Katsina: Zanga-zangar harin 'yan bindiga

"Rufe wadannan makarantu da aka yi na jihar Katsina mu a matsayinmu na masana tsaro kuskure ne, na daya ana karfafawa wadannan ‘yan ta'adda cewa gwamnati tana jin tsoronsu, saboda haka ina aka yi da wadannan yara da har wannan abu ya faru har yanzu babu tabbacin inda suke.''

Daya daga cikin azuzuwan makarantar sakandare ta Kankara da ke jihar KatsinaHoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

Wannan yankin Arewa maso yammacin Najeriya dai ya dade da fuskantar koma baya a fannin ilimin boko a kasar da ke da sama da yara da suka kai milyan 20 da ba su zuwa makaranta a yanzu. Dr Abubakar Umar Kari malami a jami'ar Abuja na mai bayyana cewa. Karin bayani: Matsalar tsaro na kara kamari a Najeriya

"Ko kadan babu tsaro saboda haka cikin kowa ya doru ruwa. Babu wani mahaifi ko wata mahaifiya da za su yarda su tura 'ya'yansu makaranta idan babu tababcin tsaro da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali. Dole ne a yi fito na fito da wadannan 'yan ta'adda a kuma murkushe su ta yadda ba su sake yin wata barazana ga tsaro da kuma zaman lafiyar al'umma ba."

Zanga-zangar iyayen yaran makarantar Chibok da har yanzu suke hannun Boko HaramHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

A bisa tsari ya kamata a ce Najeriyar ta yi karatun ta natsu da ma koyon darasi sannin cewa a irin wannan salo ne a 2014 aka sace ‘yan matan Chibok da har yanzu akwai sauran yara 112 da ba a sako su ba.

Kalo dai ya koma sama musamman a kan ‘yan majalisa da suke wakilan jama'a. Hon Mansur Ali Mashi dan majalisar tarayya ne daga jihar Katsina.

Karin bayani: Matsin lamba kan sace yara a Najeriya

"A jihar Kastina a matsayinmu na 'yan majalisa mun yi iya bakin kokarinmu mun yi ta kiraye kiraye. Abin da ya faru a garin Kankara wani abu ne mai ban mamaki. Domin gwamnatin jiha ta dauki matakai tana kuma ba da hadin kai da ma'aikatan da ke wannan shiyya, amma hakan ta faru. Ya kamata shugaban ya dauki shawarwarinmu a kawo karshen wannan matsala."

A yayin da daukacin Najeriyar ta girgizu da wannan al'amari za a sa ido a ga tabbacin da gwamnatin ta bayar ta bakin ministan tsaro Janar Bashir Magashi na ceto yaran don zama zahiri ba na fatar baka ba kawai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani