1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Damuwar 'yan siyasa a jihar Kaduna

February 24, 2026

Cece-kuce da damuwa a fagen siyasar jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya game da kamen 'yan adawa lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayansu, da iyalansu.

Nigeria, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai
Nigeria, Mallam Nasir Ahmad El-RufaiHoto: picture alliance/AA/Stringer

Dumbin magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tare da masu fafutukar tabbatar da mulkin dimukuraɗiyya a Najeriya da sauran jam'iyyun adawa, na ci gaba da nuna damuwarsu kan shafe kwanaki takwas da ci gaba da tsare El Rufa'i a hannun hukumar ICPC bisa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.

Masoyansa da iyalansa, tare da tsoffin abokan aikinsa, na kokawa kan tsawon lokacin da ya kwashe a hannun hukumar. Hajiya Hafsat Mohamed Baba, daya daga cikin ta gaba-gaban magoya bayansa, ta ce ba su ji daɗin abin da ya faru ba.

Karin Bayani:A Njeriya tsohon gwamnan Kaduna na fuskantar tuhume-tuhume

Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

A matsayin shugabanmu, tsare shi tsawon mako guda ya wuce yadda tsarin dokar ƙasa ta tanada, domin akwai dokoki da suka kayyade cewa bai kamata a tsare mutum fiye da sa'o'i 48 ba tare da gurfanar da shi a kotu ba. Amma an tsare shi kusan mako guda a ofishin ICPC.

Ta ce abin da suke buƙata shi ne adalci da gaskiya, tare da ganin an gabatar da shi a gaban kotu domin samun damar beli da kuma ganawa da iyalansa da sauran masu ruwa da tsaki. A cewarta, tsare shi na kusan mako guda ya shafi batun haƙƙin bil'adama kuma yana nuna tauye masa haƙƙinsa a matsayin ɗan ƙasa.

Mai bai wa El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar da sanarwa ga kafafen watsa labarai kan halin da tsohon gwamnan ke ciki. Ya ce lauyoyinsa da iyalansa ba su ji daɗin kin bayar da beli ba.

Karin Bayani:El-Rufai ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo

Hotunan yan siyasaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Ya ce tsohon gwamnan ya kai kansa ofishin EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026 domin amsa gayyatar da aka yi masa. 

Hajiya Hafsat ta ce suna sa ran kotun tarayya da ke Abuja za ta bi doka wajen yin abin da ya dace tare da bayar da beli, domin ba shi damar ganawa da iyalansa da kuma lauyoyinsa.

A nasa bangaren, Comrade Abdul Bako, shugaban kungiyar Campaign for Democracy, ya ce babu laifi a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu domin shi ma ɗan ƙasa ne kamar kowane mutum, amma dole ne a bi tsarin doka yadda ya kamata.

Turƙa-turƙar siyasar Kaduna na ci gaba da ɗaukar sabon salo, inda wasu jam'iyyun adawa ke kallon tsare tsohon gwamnan a matsayin bita da kullin siyasa.