Jam'iyyar APC a Najeriya ta ci zaben cike gurbi
August 12, 2018Talla
An dai fafata ne a zaben tsakanin mutum biyu daya daga jam'iyar APC mai mulki da kuma daya daga Jam'iyar adawa ta PDP. Sai dai kuma su dukka biyun 'yan gida daya ne domin kuwa mahaifinsu daya. Shugaban hukumar zaben Farfesa Hudu Ayuba Abdullahi ya bayyana sakamakon inda ya ce dan takara na jam'iyyar APC Ahmad Baba Keita ne ya lashe zaben da kuri'u dubu dari biyu da ashirin da hudu da dari shida da bakwai (224,607) yayin da Kabir Usman Baba na jam'iyyar PDP ya samu dubu hamsin da tara da dari bakwai da ashirin da hudu. (59,724)