Dillalan kayayyakin abinci sun hau teburin sulhu
March 4, 2021A cikin farkon wannan makon ne, kungiyar dillalan shanu da abinci ta shiga wani yajin aiki na dakatar da kasuwancin kai kayayyakin abincin zuwa kudancin kasar, a sakamakon kisa da asarar dukiyar da suka tafka a wasu jerin rigingimu. Akalla mutane dari da tamanin da biyar aka tabbatar sun mutu, baya ga kona motocin dakon shanu sama da dari da aka yi a yayin rikicin Shasa a jihar Oyo da kuma rikicin nan na EndSars.
Karin Bayani: Barazanar rikicin kabilanci
Abun kuma da ya bakanta ran dillalai na abincin da suka nemi diyyar Naira miliyan dubu arba'in da bakwai daga hannun gwamnatin tarayya, kafin komawa ya zuwa cinikin da ke da babban tasiri a tsakanin manyan sassan kasar biyu. Kwanakin biyar na kaurar ta abinci dai na zaman na gwajin kwanji a tsakanin sashen arewacin kasar da ke samar da abincin da kuma sashen na kudancin da ke bada kudin da masu sana'ar noman dana kiwo ke da bukata. To sai dai kuma tsadar abincin da babu irinta a sashen na kudu gami da rushewar darajarsa a dan uwansa da ke a arewa, ya tilasata komawa bisa teburi na shawara da nufin tunkarar matsalar.
Karin Bayani:Najeriya: Masu safarar abinci zuwa Kudu na yajin aiki
Daga dukkan alamu yajin aikin ya kai har ga kwakwalwa a yankin na kudancin tarrayar Najeriyar. Chif Femi Fani Kayode na zaman daya daga cikin dattawan sashen Kudu da ya taka rawa a kokarin sulhun da ya samu jagorancin gwamnan jihar Kogi Yahya Bello.Koma ya zuwa ina sulhun ke shirin zuwa a neman hanyar sauyi, ana dai kallon rikicin na da ruwa da tsaki da gwagwarmaya ta neman iko na kasar da ke rikida ya zuwa tsaron da na'isa.