Kotu ta bai wa el-Zakzaky izinin zuwa neman magani
August 5, 2019Talla
Lauyoyin malamin ne suka nemi a bai wa malamin izinin fita bayan da ya shafe shekaru a tsare cikin yanayi na rashin lafiya. A shekarar 2015 aka kama malamin tare da mai dakinsa a yayin wani artabu a tsakanin mabiyansa da rundunar sojin Najeriya a garin Zariya da ke jihar Kaduna a arewacin kasar.
Tun daga wancan lokacin mabiya malamin ke gudanar da gangami don janyo hankalin gwamnati na sakin malamin ba tare da anyi nasara ba. A lokuta da dama da ake gudanar da ire-iren wadannan gangamin, an yi ta samun barkewar rikici da ke janyo asarar rayuka.