Igbo da Yarbawa na fafutukar neman balewa
July 29, 2021
Yanzu haka dai gwamnatin Najeriya na tsare da Nnamdi Kanu jagoran kungiyar IPOB ta 'yan kabilar Igbo sobada da'awar da yake ta neman balewa domin kafa kasar Biafra. Yayin da a share daya hukumomi a Jamhuriyar Benin suka kame Sunday Igboho dan kabilar Yarabawa shi ma mai fafutukar neman ganin yankin na Yarabawa ya bale. Hukumomin na Benin sun samu Sunday Igboho da laifin mallakar fasfo biyu. Kamen na Igboho da ke kan hanyar tserewa zuwa kasar Jamus dai na zaman babbar nasara ga gwamnatin tarrayar Najeriya da ta yi nasarar cafke madugun awaren Biafra Nmandi Kanu a watan Yuni. Mutanen guda biyu dai na zaman na kan gaba a kokarin kare shekaru dari da doriya na rayuwar tarrayar Najeriyar sun kuma share tsawon lokaci suna gwada kwanji da fadar gwamnatin kasar. Mun tanadar muku da rahotanin a kasa dangane a wannan batu.