Najeriya: Farfagandar yaki da cin hanci gabanin zabe
January 31, 2019Talla
Atiku Abubakar din dai ya ce yana da niyyar sauyin tsarin yaki da cin hancin Najeriya tare da yin afuwa ga barayin biron da suka amince domin dawo da kudaden. A fada ta madugu na adawar dai wannan tsari ya yi aiki a tsohuwar gwamnatin kasar inda suka dawo da sama da Dalar Amirka miliyan dubu hudu, sannan kuma yana zaman kashin bayan sake ginia Turkiya. Duk da cewar dai tsarin ya yi aiki a tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo, daga dukkan alamu kuma ya gaza ga gwamnatin Yar ‘Aduwa da ma 'yar uwarta ta Jonathan da ta shude a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban kungiyar Transparency reshen Nigeria mai yakar cin hanci a kasar.