1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare sun kara ta'azzara a Najeriya

October 31, 2022

Majalisar tsaron Najeriya ta ce ta kama mutane da yawa a kokarin kai karshen barazanar rashin tsaro cikin kasar a halin yanzu.

Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

An dai dauki kwanaki idanu bude a mafi yawa na sassan tarrayar Najeriya dake fuskantar barazanar rashin tsaro cikin kasar a halin yanzu. Shawarwarin kasashen yamma ne dai suka kai ga sabuwar barazanar da ta kalli sake maida kasar zuwa karatun baya cikin rashin tsaron.

To sai dai kuma wani taron gaggawar majalisar tsaron kasar ta ce ta kama da daman gaske a kokari na kwantar da hankula anan a Abuja dama sassa daban daban a tarayyar Najeriyar.

Bayan kamalla wata ganawa ta tsawon kasa da awa guda, mashawarcin tsaron kasar Babagana Monguno yace jami'an tsaron kasar sun kame da dama cikin samamen da suke kaiwa yanzu.

Babagana Monguno da Abayomi Olonisakin Hoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma

Ina son baiwa yan Najeriya tabbacin cewar al'amura sun lafa a halin yanzu. Jami'an asiri da na tsaro sun kama da daman gaske, kuma ana nazarin abubuwan da suka bankado ya zuwa  yanzu. Ba al'adarmu  ba  ce baiyana ko me ake yi, amma mafi muhimmanci shi ne tun daga lokacin da aka fara wannan batu daga mako daya zuwa kwanaki 10 da suka gabata,  ya zuwa  yanzu, in kun lura abubuwa sun kwanta.

 Batun a tsorata yan Najeriya abu ne maras dalili, abubuwa a wurare daban daban a nan babban birnin tarraya sun kwanta, kuma muna kokari na aiki da makwabtanmu, sannan kuma a tsarin diplomasiya muna  aiki da abokanmu a cikin mutunci, ba tare da nuna cewar tarrayar Najeriya na rawa cikin makabarta kuma ta sha ka fashe karya ne, kuma rashin mutunci ga wani ya nuna irin wannan alama.


Kokari na neman mafitar rashin tsaro ko kuma kokari na kwantar da hankali na yan kasa, in har Abujar tai nasarar tsira daga masu ta'addar, da kyar da gumin goshi wani barikin sojoji a garin Wawa ya sha daga masu ta'addar da ke kokari na kwatar nasu.

A wani abun da ke nuna alamun ta maza a bangare na masu ta'addar da a tsakiyar shekarar bana su kai nasarar kwance nasu dake daure a kurkukun garin Kuje dake babban birnin tarayya na Abuja. To sai dai kuma babban hafsan tsaron kasar Janar Lucky Irabor dai ya ce akasin abun da ya faru can a Kujen sojojin kasar sun farka.

Shugaba Buhari da hafsoshin tsaron NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

“Sojojinmu da  'yan sanda  da   sauran jami'an tsaro na aiki babu dare ba kuma rana da nufin tsare rayuwa da dukiyar al'umma ta kasa. Ba wani batu na tada hankali, yan najeriya su cigaba da harkokinsu na yau dana gobe. Kamar yadda kuka sani a ranar 29 ga watan nan an kai hari a barikinmu na Wawa dake jihar Niger.Amma kuma fargar jami'anmu ta sa mun mai da martani tare da kashe maharan tare da kame motarsu dake makare da boma bomai, mun kuma mutane biyar cikin masu hari.”

To sai dai kuma a yayin da jami'an tsaron kasar suke fadin sun nasarar kau da harin daga dukka na alamu kuma shawarin kasashen yamman  na shirin jawo rikici a tsakanin tarrayar Najeriya da kawayenta na gado.

 Ministan harkokin wajen kasar  Geofry Onyeama dai ya ce gwamnatin tarayyar Najeriyar na shirin jan kunne na kasashe na waje da su kauce wa duk wani abun dake iya tada hankali cikin kasar a cikin suna na shawara.

“Ma'aikatar harkokin waje da kuma jami'an asirin tarrayar Najeriya na aiki tare da nufin tunkarar matsalar da kuma hada kafada da abokanmu dake waje da nufin rage kaifin duk wata barazanar da ke shirin shigowa a waje sannan kuma da tabbatar da cewar duk abun da za'ayi ko a fada to yana iya taimakawa tarrayar Najeriya ne maimakon jawo matsala ko kuma ruda daukaci kasar ta kowane hali.”

'Yan kwanakin da ke tafe dai na da tasirin gaske ga tarayyar Najeiryar da ma ragowar kasashen Afrika da sannu a hankali ke dawowa daga rakiyar kawancen dake tsakaninsu da yamma, amma kuma ke kallon tasirin karkata ta hankalin a cikin kokon shansu.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani