1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hare-haren Boko Haram a Monguno da ke Bornon Najeriya

January 8, 2020

Ana fargabar an samu asarar rayuka bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a Monguno da ke arewacin jihar Borno kwanaki bayan janyewar sojojin kasar Chadi daga yankin.

Nigeria Baga | Truck des IS Gruppe (ISWAP)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Da yammacin ranar Talata mayakan da ke alaka da kungiyar ISIS suka nufi garin na Monguno, inda suka kasu kashi biyu wasu suka yi kwantan bauna ga tawagar sojojin Najeriya da ke kan hanyar zuwa garin, inda wasu kuma suka afka wa garin ta wasu jerin gidajen da ma'aikatan jin kai ke zaune a ciki wanda ake kira 20 Housing Unit.
An dai kwashe lokaci ana bata-kashi tsakanin sojojin da mayakan, inda wadansu suka shiga garin Monguno ta da ta bangaren suka bude wuta irin na kan mai uwa da wabi, abin da ya sa mutanen garin gudu domin tsira.


To sai dai babu cikakken bayani na yawan mutanen da hare-haren suka rutsa da su, amma wasu rahotannin da ba na hukumomi ba sun ce akwai sojojin Najeriya uku da suka riga mu gidan gaskiya wasu kuma sun samu raunuka.
A bangaren fararen hula kuma babu adadin alkaluma na yawan wadanda harin ya rutsa da su, inda karancin hanyar sadarwa ya hana samun cikakken bayanai.


Sai dai mazauna garin da suka tsere sun bayyana cewa an cinna wuta a sansanin 'yan gudun hijira na garin wanda yake makarantar sakandare da ake cewa GSS Monguno da kuma kwashe kayayyaki a gidajen ma'aikatan jin kai da suka tsere saboda harin. Ana alakanta wadannan sabbin hare-hare da janyewar sojojin kasar Chadi bayan cikar wa'adinsu na zama a Najeriya ya zo karshe a makon da ya gabata.

Sojojin Chadi a fagen yaki da Boko Haram a kan iyakar Chadi da NajeriyaHoto: Reuters/E. Braun


A cewar masu fashin baki abin kunya ne a ce janyewar sojojin zai haifar da gibi da har mayakan Boko Haram za su kai hari wanda a baya lokacin da sojojin na Chadi ke nan ba a kai irin harin ba. Malam Adamu dan Borno wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a cewarsa kai wannan hari na nuna an samu gazawa daga bangaren sojojin Najeriya.


"Wannan abin in ka duba shi da idon basira abu ne kusan abin kaskanci ne ga gwamnatin Najeriya, har a ce wai yau gwamnatin Najeriya ba ta da sojan da mutanen Najeriya suka aminta da su, sai sojan Chadi ko na wata kasa. Gaskiya wannan abin kunya ne a gare mu, abin takaici ne a gare mu. Rigingimun da ake yi a Najeriya ne a ce wai don sojan Chadi sun janye mutane suna gujewa muhallansu, suna barin gidajensu, to gaskiya wannan abin bai yi tsari ba ko kwata-kwata."


Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta bayyana cewa babu dalilin da zai sa jama'a su tada hankulansu saboda janyewar sojojin kasar Chadi a bangaren Najeriya tare da bada tabbacin cewa za a maye gurbinsu da sojojin kasar da za su tabbatar da tsaro a yankin. Amma da alamu wannan magana ba ta shiga kunnuwan mazauna Monguno da sauran garuruwa da ke wuraren da sojojin Chadin suka janye ba, don kuwa da samun labarin kai hari garin da kuma karajin harbe-harbe ya sa mutane da dama gudu daga garin zuwa wuraren da suke ganin tudun na tsira ne ciki har da birnin Maiduguri.

Yanzu haka an tsaurara matakan tsaro, ana kuma ganin jami'an tsaro sun ja daga a wurare abin da ake ganin bai rasa nasaba da zanga-zangar da kungiyoyin fararen hula suka shirya yi domin nuna damuwar kan dawowar hare-hare daga bangarorin mayakan Boko Haram a 'yan kwanakin nan.
Babu dai wata sanarwa da ta fito daga bangaren gwamnati ko jami'an tsaro kan wannan hari da kuma yunkurin kungiyoyin fararen hula na yin zanga-zangar nuna damuwa da hare-haren.