1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin makiyaya a Najeriya na sa fargaba

Uwais Abubakar Idris LMJ
January 25, 2021

A Najeriya kungiyar sasanta mabiya addinai domin tabbatar da zaman lafiya ta nuna damuwa a kan rikicin da ya taso tsakanin Fulani makiyaya da wasu al'ummomin jihohin Kudu maso Yammacin kasar.

Nigreria Fulani-Nomaden
Zargin Fulani makiyaya da garkuwa da mutaneHoto: AFP/Luis Tato

A kwanakin baya-bayan nan, hatasaniya ta barke tsakanin Fulani makiyayan a wasu jihohin Kudu maso Yammacin Najeriyar musamman ma jihar Ondo, biyo bayan wa'adin da gwamnan jihar ya bai wa Fulani makiyayan yana mai bukatar su fice daga jihar. Wannan mataki dai da ya tayar da hankalin kungiyar Mabiya Addinai da Wanzar da Zaman Lafiya ta Najeriyar, tare ma da yin kashedi ga masu neman tayar da fitina.
Bishop Sunday Onuoha shi ne shugaban kungiyar bangaren mabiya addinin Kirista: "Ni nasan wahalhalun da muka dandana a lokacin yakin basasa, mun sha azaba ta rashin muhali da yunwa. Ba wanda zai yi fatan wannan hali ga kowa koda kuwa makiyinka ne in kana da shi, don haka in muka ga mutane na kada kugen yaki suna furta kalamai na da ke tada wutar rikici a Najeriya, wannan na bani takaici. Wannan lokaci ne da  ya kamata shugabanni da mutanen gari su ceto Najeriya daga hannun wadanda ba su san ya kamata ba.''

Rikici a Najeriya na haddasa asarar rayuka da dukiyoyiHoto: AFP/Luis Tato

Karin Bayani:Mayar wa Fulani burtalai a Jigawa

Nuna dan yatsa a kan Fulanin makiyaya na zargin garkuwa da mutane tuni ya sanya wasu jihohin da ke Kudu maso Yammacin Najeriya suka kama hanyar bin sahu a kan wannan matsala na bukatar Fulani makiyaya su bar yankin nasu, duk kuwa da kashedin da shugaban Najeriyar ya yi a kan haramcin hakan. A yayin da wa'adin da gwamnan jihar Ondon ya dibawar Fulanin ke cika a wannan Litinin din,  bayanai sun ce ana can ana tattaunawa tsakanin gwamnonin jihohin Kudu maso Yammacin Najeriyar da shugabanin Fulani makiyaya a kan wannan lamari.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani