1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar rikici a zaben 2023 a Najeriya

November 28, 2022

Fargabar barazana ga makomar zabukan badi a Tarayyar Najeriya, sakamakon ci gaba da kai hari a cibiyoyin zabe na kasar duk da alkawari na bayar da kariya ta kadara da cibiyoyin zaben.

Najeriya | Zabe | INEC
Fargabar yiwuwar samun barazana a Najeriya, yayin zaben 2023 da ke tafe Hoto: Reuters/A. Sotunde

An dai sha alwashi na bayar da kariya cikin harkar zabe, amma ce ana shirin tura soja da sauran jami'an tsaro a ofisoshin zaben. To sai dai kuma ana kallon karuwar hari a kan kadarorin zabe a Najeriyar a halin yanzu, na baya-baya dai na zaman wani sabon hari a cikin wannan mako a ofishi nan Hukumar Zaben da ke a jihar Ebonyi. Harin  da ke zaman na uku cikin tsawon kasa da wata guda, na kara fitowa fili da sabuwar  barazanar da zabukan kasar ke fuskanta. Zainab Aminu dai na zaman kakaki ta Hukumar Zaben da ta ce, ana bukatar damara mai girma domin iya bayar da kariyar da ake da bukata yayin zaben. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin Hukumar Zaben da jami'an tsaron da ke da alhakin kare zaben dai, karuwar harin na kara fitowa fili da sabuwwar barazana kan yiwuwar zaben a cikin Tarayyar Najeriyar.  Zaben na badi dai na zaman na farko da ake hasashen shirin darma sa'a, sakamakon amfani da fasaha a cikin tsarin da ya saba da magudi can baya.

Batun shirin amfani da na'ura ya janyo cece-kuce a NajeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP

Sanata Umar Tsauri dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar PDP ta adawa, kuma ya ce tsoron faduwa a yayin zaben ne ya sanya kona kadarorin zaben. Tarrayar Najeriyar dai na fuskantar yanayin zaben da ke dada kallon rabuwa ta masu takara kan turbar addini da kabila,  abun kuma da da ke kokarin jefa zaben na badi da kila ma makoma ta kasar cikin tsaka mai tsananin wahala. Ta'azzarar hari kan kayan zaben da ya zuwa yanzu ke zaman ruwan dare a sashen kudancin Najeriyar a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan al'amuran siyasa, na iya yaduwa zuwa sashen arewacin kasar da kila jawo damuwa kan makoma ta kasar. Tuni dai da ma aka fara ruwaito wasu a cikin jiga-jigan siyasar Najeriyar, na korafi kan sabon tsarin fasaha da 'yan kasar ke kallon na iya kai wa ga sahihin zabe. A baya dai kasar ta dauki lokaci tana mai karfi sai Allah, a cikin tsarin da ya rika kallon sanar da sakamkon zaben tun ma kafin kai wa ya zuwa kamalla kirga.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani