1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fulani na zaman zullumi a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 4, 2021

A Najeriya Fulani makiyaya na cikin zullumi, a jihohin Oyo da Edo da ke sashen Kudu maso Kudancin Najeriya da kuma Abiya da Ebonyi a yankin Kudu maso Gabas. 

Cartoon Nomadenkrise Nigeria
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci makiyaya su zauna a gidaHoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

A yayin da  Fulani makiyaya ke ji ba dadi a sassa dabam-dabam cikin Tarayyar Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ta kaddamar da bincike da nufin tabbatar da kariya ga Fulanin da ma daukacin 'yan kasar da ke fuskantar barazana a halin yanzu. A yankin Kudu maso Kudancin kasar dai, wasu gungun mata ne na yin zanga-zangar neman korar Fulani daga yankinsu.

Can ma a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar, Fulani makiyayan na ji a jiki sakamakon kona gidaje da karkashe musu dabbobbi a wsu jihohi biyu na yankin, a wani abun da ke dada nuna irin girman barazanar da kabilar ta Fulani ke fuskanta.
Halin da Fulani makiyayan suka tsinci kansu a ciki ne dai, ya sanya gwamnan jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar, wanda shi ma ke zaman Bafultani yin kira ga makiyayan da sua daina fita zuwa wasu sassan kasar domin kiwo.

Sai dai tuni kiran nasa ya fuskanci martani daga shugabannin kungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriyar. Sannu a hankali dai rikicin makiyaya da manoman na neman rikidewa zuwa barazana mai girma a cikin Najeriyar da ta dauki lokaci tana neman hanyar tunkarar rashin tsaro.