1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadi ga masu zanga-zanga a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2024

Rundunar sojojin Najeriya ta gargadin kaucewa kwaikwayon tsarin tayar da tarzoma na masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Kenya, a daidai lokacin da aka shirya yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a kasar a makon gobe.

Najeriya | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa | Sojoji | Gargadi
An jima ana kokarin yin zanga-zanga kan tarin matsalolin da Najeriyar ke cikiHoto: SAMUEL ALABI/AFP

Yayin da masu zanga-zanga a Kenya suka cimma nasarar tilasta gwamnati ta janye sabuwar dokar haraji, a Najeriya ba a fuskanci wani gagarumin tashin hankali kan bukatar gyara a tsarin tattalin arzikin kasar da ya tilsta tashin gauron zabin farashin kayan abinci da kaso 40 cikin 100. Tuni dai taken zanga-zanga na "EndBadGovernanceinNigeria" da kuma "RevolutionNow" ke ta yin tshe a shafin X, tare da yin kira ga 'yan Najeriyar su fito kan tituna daga ranar daya ga watan Agustan da ke tafe domin gudanar da jerin gwano.