1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Gwamnan Kano ya koma jam'iyyar APC

Nasir Salisu Zango SB
January 26, 2026

A jihar Kano da ke Najeriya an bude sabon shafi a hukumance bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi sabuwar tafiyar jam'iyyar APC mai mulkin kasar, yayin wani biki a fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ke Najeriya
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ke NajeriyaHoto: Nasiru Salisu Zango

Bayan tsahon lokaci yau ta tabbata Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ke Najeriya ya zama dan jam'iyyar APC mai mulkin kasar. Yayin wani biki da ya samu halartar manyan jiga-jigan jam'yyar APC na kasa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya shiga jam'iyyar APC domin samar da mafita da kawo hadin kai da ci-gaba ga mutanen jihar Kano, gwamnan ya yi kira da samun hadin kai da kuma alkawarin ci gaba da dora Kano bisa gwadaben ci-gaba mai dorewa.

Takun saka bayan sauya sheka

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ke Najeriya da Rabiu Musa Kwankwaso kafin raba gariHoto: Nasiru Salisu Zango

Tuni dai yan jam'iyyar APC ke murna da wannan yanayi, sannan asu bin shahadar gidan Madugu ke ci gaba da nuna bakin cikin bisa yadda suke ganin an musu ta leko ta koma, Dr Yusuf Kofar Mata na daga cikin kwamishinoni da suka ajiye aiki suka bi madugu ya bayyana dalilin su na kin shiga jamiyyar APC, saboda suna ganin haka a matsayin abin da ya saba hakidar da suke kai.

Zuwa yanzu dai ana ta samun sauye-sauye tsakanin magoya baya da wasu ke bayyana matsayinsu na kasancewa da Madugu a tsohuwar tafiya. Yayin da wasu ke bin gwamna a tsunduma cikin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. Mataimakin shugaban Majalisar dattijan Najeriya Barau Jibril ne ya daga hannun gwamna cikin yanayin cewar ka dawo gida cikin jam'ioyyar APC.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani