1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin fadada sufurin jiragen kasa

September 24, 2020

 A kokarinta na inganta harkokin sufuri a kasar, gwamnatin Najeriya ta ce za ta gina sabon layin dogo na zamani mai tsawon kilomita 248 a arewacin kasar da zai hade da makwabciyarta ta Jamhuriyar Nijar. 

Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Hoto: DW/U. Musa

Layin dogon dai zai hade biranen Kano da Katsina da Dutse a Najeriya kafin tsallakawa zuwa Maradi da ke kudancin Jamhuriyar Nijar. Ana dai kallon aikin da Najeriyar ta ce zai lashe dalar Amirka kusan miliyan dubu biyu a matsayin sabon yunkuri na tabbatar da gammaya a cikin yankin yammacin Africa da ke da bukatar habbaka ciniki da zamantakewa tsakanin al'ummarsa.

Ministan sufuri a Najeriya Rotimi Ameachi ne dai ya sanar da amincewar majalisar zartarwar kasar na bada wannan aiki wanda shi ne irinsa na Uku da yanzu haka ke kan layi, bayan na Ibadan zuwa Kano da kuma Fatakwal zuwa Maiduguri da ke bukatar dubban miliyoyi na daloli daidai lokacin da kasar ke korafin rashin kudi.

Tuni dai masana a Najeriya ciki kuwa har da Auwal Mu'azu suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon aiki, anda Malam Auwal din ke ganin aikin a matsayin wata alama ta amincewa da tsarin ciniki na bai daya na nahiyar Afirka wanda ke da tasirin gaske ga kasashen na Najeriya da Nijar. Har wa yau, aikin inji shi zai taimaka wajen samawa al'umm aikin yi a kasashen biyu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani