1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan yaki da cin-hanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 12, 2023

Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na kara kaimi a yaki da cin-hanci da rashawa tun bayan ranatsar da shi, inda aka ga an fara kamo mutanen da ake zargi da aikata ba daidai ba a kasar.

Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu
Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Makwani biyu kenan cur da  hawa karagar mulkin Najeriyar, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakai da ke nuna kamun ludayinsa a kan batun yaki da masu cin hanci da rashawa a kasar. Kama  daga tsohon gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya zuwa tsohuwar ministar kula da harkokin mata ta Najeriyar Pauline Tallen da dakarar da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele wanda yake tsare a kan zargi na cin-hanci da rashawa, matakin da shi ne ya fi daukar hankalin 'yan Najeriya da mau masu rajin yaki da cin-hanci da rashawa. Duk da cewa har zuwa wannan lokaci bai kai ga kafa majalisar zartaswa ba, amma sabon shugaban na Najeriya  ya mayar da hankali a kan wannan matsala da ta zama dalilin koma bayan tattalin arziki da zamantakewar alumma.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da aka cafke Godwin EmefieleHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Tuni dai wasu kungiyoyin farar hula da ma lauyoyi ke bayyana rashin  hallaci ko taka doka, a kan kame gwamnan babban bankin Najeriyar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta yi. Amma ga masana tattalin arziki kamar Yusha'u Aliyu na ganin yadda al'amuran tattalin arzikin Najeriyar suka gudana a karkashin kulawarsa, dole ne zargi ya biyo baya. Har zuwa wannan lokaci dai yana hannun hukumar tsaro ta farin kaya yayainda ita kuma tsohuwar ministara kula da harkokin mata ke hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa inda suke amsa tambayoyi. Yan Najeriya na cike da fatan dorewar matakai na yaki da masu halin bera da suka yiwa tattalin arzikin kasar mumunar illar da ta jefa milyoyi cikin hali na ‘yan rabanna ka wadatamu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani