Najeriya: Ana ci gaba da tsare yara 'yan zanga-zanga a Borno
November 15, 2024Gwamnatin Jihar Borno ta bakin kwamishinar shari'a kuma Babbar lauyar gwamnati ta jihar Barista Hauwa Abubakar ta shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa duk wadanda aka gabatar a gaban kotu da wannan tuhumar da ake yi musu da cin amanar kasa baligai ne wanda suka san ciwon kan su.''Tun farko ma mun yi taro da Kwamishinan ‘yan Sanda, babu kananan yara a cikin wadanda aka kama ake tuhuma wadanda aka samu ba su da laifi an kai su wuraren da za a kula da su amma a hakikanin gaskiyya tun farko babu wani karamin yaro da bai balaga ba wanda aka tsare a dukkanin wuraremun da ake tsare mutane.''
To sai yanayin ya sha bam-bam da abin da aka shaida a kotu lokacin da aka gabatar da wadanda ake tuhumar su da laifin cin amanar kasa don kuwa akwai wadanda aka tabbatar da cewa yara ne da ba su balaga ba wadanda shekarun su ya kama daga 14 zuwa 17. Iyaye da masu kare hakkin yara wanda sun tabbatar da cewa akwai kananan yara wadanda Alkali mai shari'a Aisha Mohammed Ali ta babban kotu jihar ta 10 ta ba da umurnin a tsame su tare da kai su gidan kula da kangararrun yara inda sauran aka mayar da su gidan gyara hali.
Barista Yakubu Alhaji Adamu daya daga cikin lauyoyi ne da ke tsayawa wasu daga cikin wadanda ake tuhuma da aka gabatar a gaban kotu ranar 4 ga wannan watan. ''Mu za mu fara duban abin ne a mahanga ta yadda abin ya zo gaban kotu. A takarda da aka kawo gaban kotu shi ne yaran nan, an samu masu shekara 17 zuwa 18 ne, amma da a ce duniya za ta kalle su a zahiri akwai wanda gaskiyya bai wuce shekaru 14 ba.''
Suma kungiyoyin kare hakkin yara da masu rajin kare hakkin bani Adama sun tabbatar da cewa a cikin wadanda ake tuhuma a ka gabatar su a gaban kotu ranar 4 ga wannan watan Nuwamba akwai kananan yara da ba su mallaki hankalin kan su ba. Abin jira a gani dai shi ne ko za a janye wadannan yara daga cikin wannan shari'a tare da soke tuhumar da ake musu kafin ranar da kotun za ta ci gaba da sauraron karar wato ranar 18 ga wtan Nuwamban wannan shekara? Lokaci kawai zai tabbatar.