1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Komawa aikin hakar man Najeriya a Ogoni

September 25, 2025

Bayan shafe shekaru 32, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana aniyarta ta sake komawa yankin Ogoni mai arzikin man fetur

Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Man Fetur | Shell | Ogoni | NNPC
Aikin haka da tace man fetur, na taka rawa wajen gurbata muhalliHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Aikin hakar man fetur a yankin na Ogoni dai, wamnatin  ya dakata tun a shekara ta 1993. Kimanin gangar danyen mai dubu 28 yankin na Ogoni ke samarwa, kafin wani rikici tsakanin kamfanin mai na Shell da mazauna yankin ya tilasta tsai da aikin hakar man.

Ogoni na zaman daya daga cikin na kan gaba, a yankunan da ke samar da babbar hajar da kasar ta dauki lokaci tana kallo da idanun kima. Abujar dai na kallon man na Ogoni da fatan cike gibin gangar mai miliyan biyu, abin da kasar take da fatan ta haka kullum.

Karin Bayani:Shekaru 20 bayan kisan Ken Saro-Wiwa

Kuma wani kokarin sulhunta  tsakanin dattawan na Ogoni da gwamnatin  kasar, ya kare da hukuncin sake komawa yankin da nufin ci gaba a cikin aikin da ke da fatan sake dora man na kan gaba cikin kudin shigar 'yan mulki.

Hakuri da manta baya

Aikin tsaftace yankin Ogoni na Najeriya

03:22

This browser does not support the video element.

Abun kuma da ya burge shugaban kasar da ke neman hanyar tara karin kudin shiga, ya kuma bai wa wasu dattawan na Ogoni hudu  lambobin girma. "Ina rokon al'ummar Ogoni a daukacin garuruwan yankin da su manta da banbamcin da ke a tsakaninsu, su dora mummunan tarihinsu a bayansu su ci gaba a matsayin al'umma daya da ke da hadin kai....." A cewar shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu.

Koma ya zuwa yaushe Abujar ke shirin ta kai cikin sabon tarihin na Ogoni dai, har ya zuwa yanzu tana gwa-gwa-gwa da wani shirin yasar dagwalon man fetur da kamfanin Shell na hakar mai ya bari a cikin yankin.

Sama da murabba'in kilomita 1000 na gurbataccen man ne dai, ya lalata wasu kauyuka 261 a cikin yankin. Farfesa Don Baridam dai shi ne shugaban wani kwamitin da ya jagoranci kokarin sulhunta tsakanin juna, kuma ya ce: "Batun muhalli a yankin na zaman na kan gaba, a kokarin sabon sulhun da ma sake fara aikin na hakar mai a cikin yankin....."

Kalubalen muhalli

Sama da dalar Amurka miliyan 1000 ne dai kamfanin na Shell ya kai ga batarwa a cikin yankin, amma kuma ba tare da samun tasirin da ake da bukata a cikin aikin yasar dagwalon man fetur din ba. Bayan Ogoni, yankuna da dama a Niger Delta na fuskantar matsalar gurbatar muhallin sakamakon karuwa fasa bututu da kila satar man fetur.

Karin Bayani:Kaddamar da shirin tsabtace Ogoni

Injiniya Mohammed Lawal tsohon darakta ne a kamfanin man NNPC na kasar, kuma ya ce: "Ko bayan rikicin na Ogoni da akwai sauran tafiya, tsakanin Tarayyar Najeriyar da warware rigingimun da ke tsakanin al'ummar yankin......"

Ya zuwa shekara ta 2018 Najeriyar dai, ta yi asarar da ta kai Naira Triliyan dai-dai har 63 daga tsai da aikin na hakar man na Ogoni. Yankin kuma da ya zuwa shekara ta 1992, ke samar d aganga dubu 28 na man kusan kullum.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani