Ta'addanciAfirka
Halaka tsageru takwas a Najeriya
September 16, 2025
Talla
Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa dakarun kasar sun halaka sun halaka tsageru masu kaifin kishin addinin Islama takwas ciki har da shugabannin tsagerun na kungiyar ISWAP, lokacin dauki ba dadi a yankin arewa maso gabashin kasar.
Rikici na tsawon lokaci
A wannan Talata rundunar sojan ta ce lamarin ya faru a jihar Borno, inda aka dade ana samun kungiyoyin jihadi.
Gwamnatin Najeriya tana fama da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP, inda dubban mutane suka halaka kana wasu da dama suka rasa matsugunansu, sakamakon artabu tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kungiyoyin tsagerun masu ikirarin jihadi cikin yankin arewa maso gabashin kasar.