SiyasaAfirka
An kai hari kan gidan yari a Imo
April 6, 2021
Talla
Wata sanarwa daga ma'aikatar gandiroban kasar ta fitar, ta ce da misalain karfe biyu da mintoci 15 na tsakar daren Litinin ne wasu mutane dauke da muggan makamai suka kai harin tare da sallamar fursunonin da ke tsare a gidan yarin, sai dai mai magana da yawun hukumar gidan yarin ya bayyana cewa an shawo kan matsalar.
Ita ma dai Jihar Abia mai makwaftaka da Imon, ta kakaba dokar hana fitar dare daga karfe 10 na daren jiya zuwa karfe shida bisa fargabar abinda ka iya faruwa.
Shugaba Mahamadu Buhari ya yi Alllah wadarai da harin, yana mai kwatwanta wadanda suka kai shi a matsayin 'yan ta'adda.