1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan Ambazoniya na kai hari Najeriya

Muhammad Bello LMJ
December 14, 2023

'Yan awaren kasar Kamaru da ake kira da 'yan Ambazoniya sun afkawa wasu kauyukan a jihar Cross River da ke makwabciyar kasa Najeriya, daga bangaren Tsibirin Bakassi da ya raba jihar da kasar ta Kamaru.

Najeriya | Cross River | Hari | Kamaru | Ambazoniya
Jihar Cross River da ke Tarayyar NajeriyaHoto: Michael Runkel/imageBROKER/picture alliance

Yayin harin 'yan awaren Ambazoniyan a jihar Cross River da ke makwabciyar kasa Najeriya da ya halaka mutane da dama, sun kuma yi awon gaba da mata da kananan yara. Kawo yanzu dai mahukuntan Najeriya ba su ce komai ba kan batun, koda yake mataimakin gwamnan jihar ta Cross River Peter Odey ya kai ziyarar jaje yankunan da abin ya afku da ke tsukin Belegete a cikin karamar hukumar Obanliku a jihar ta Cross River mai makwabtaka da Kamarun ta kan iyakar Tsibirin Bakassi. Rahotanni sun nunar da cewa ba wannan ne karon farko da harin ya afku ba cikin wata guda, amma harin na baya-bayan nan ya halaka sama da mutane 30 a kayukan da suka kai samamen musamman ciki har da shugabanninsu da dama.

Yadda sojan Kamaru ke yakar 'yan aware

03:35

This browser does not support the video element.

Al'ummar jihar ta Cross River dai, na yawan samun barazana daga 'yan awaren na Ambazoniya da ke Kamaru, gwamnatin jihar ta ce tana fuskantar kawarara 'yan gudun hijira daga Kamarun da ko a yanzu yawansu ya kai dubu 52 wadanda ke tserewa hare-haren 'yan awaren na Kamaru. Yawancin kauyukan jihar ta Cross River da 'yan Ambazoniyan kan afkawa dai na gabar ruwa ne, inda suke shiga ta hanyar amfani da kananan jiragen ruwa masu dan karen gudu. Koda yake an nunar 'yan bindugar IPOB na Najeriya da kan yi kara-kaina a wannan tsuki kan takalo 'yan Ambazoniyan, abin da ke janyo harin ramuwar gayya da kauyawan wannan tsukin ke kwana a ciki.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani