1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Illar ficewar kamfanonin waje ga kasa

Uwais Abubakar Idris
January 23, 2024

A Najeriya ficewar da kamfanonin kasashen waje ke yi daga kasar saboda matsaloli mabambanta ya sanya kasar asarar tiriliyan uku na kudin shiga

Kamfanin hakar mai a Najeriya
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/G. Esiri

 Abu ne da ya faro kamar wasa inda kamfanonin kasashen waje da ke gudanar da harkokinsu suka fara zurarewa suna barin Najeriyar. Daya bayan daya kamfanonin 22 ne suka fice daga kasar a tsakanin 2021 zuwa 2023. Dukkaninsu bisa dalilai mabambanta da suka hada da rashin wutar lantarki da tsadar man diesel, da kuma rashin tsaro. Ficewar da ta zama lamari mara dadi ga Najeriyar. Mallam Yushau Aliyu masani a fanin tattalin arziki ya bayyana man fahimtarsa kan dalilan da suka haifara da hakan.

Hoto: Abedin Taherkenareh/epa/dpa/picture alliance

"Manyan abubuwan da ke haifar da wannan sun hada da yadda ake kasuwanci a kasar, ana bari ana shigo da kayayyaki masu arha fiye da wadanda ake samarwa a cikin gida, sannan ga matsala ta rashin tsaro. Domin tun shekaru uku da suka gabata muke ganin kamfanonin na ficewa suna barin kasar saboda matsalolin fitar da ribar da suka samu a kasar''.

Na baya baya nan daga cikin kamfanonin da suka fice shine Uniliver da ya sanar da dakatar da samar da kayyakin da ake amfani da su a gida a shirye shiryen tattara kayansa ya fice. Tun kafin wannan akwai kamfani irin su Procter and Gamble, GSK da Pernoid da suka yi gaba. Bayanai daga kungiyar tuntubar juna ta ma'aikata ya nuna cewa ma'aikata dubu 20,000 ne suka rasa ayyukansu dalilin wannan.

Hoto: picture-alliance/dpa/Göttert

Hatta masu masana'antu na cikin Najeriya sun dade suna kokawa a kan halin da suke ciki na wahalhalun gudanar da ayyukansu. 

Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya lallashi kamfanonin da su nuna hakuri su bar ficewa daga kasar. Ministan ciniki da masana'antu na Najeriyar Niyi Adebayo ya bayyana cewa akwai matakan gyara da ake dauka.

Kungiyar tuntubar juna ta ma'aikata ta bayyana damuwa a kan wannan hali da ke kara haifar da rashin aikin yi da ya kai sama da kashi biyar cikin 100 na ‘yan Najeriyar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani