1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Illar yawan kudade a hannun Jama'a

Uwais Abubakar Idris
January 31, 2024

Babban bankin Najeriya ya nuna damuwa kan yawan kudadden da ke hannun jama'a wadanda basa ajiya a banki ya kai kasha 92 cikin 100 na tattalin arzikin kasar yayin da ake fuskantar hauhawan farashin kayayyaki a kasar.

Nigeria Geldwechsler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Karuwar yawan kudadden da ke jujuyawa a hannun jama'a wadanda ke tattalin arzikin kasar da ya kama daga Naira tirliyan N2.7 zuwa Naira triliyan N3.3 da babban bankin kasar ya bayyana cewa a yanzu kashi 92 cikin 100 na wadannan kudadden basa a bankunan kasar, suna hannun jama'a, inda mutane da yawa suka mayar da gidajensu tamkar bankuna. Dr Isa Abdullahi masanin tattalin arziki a Abuja ya ce hakan na da matukar illa ga tattalin arzikin kasa

Kudin Naira na NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wannan yanayi da ake ciki ya sanya babban bankin Najeriyar shiga mawuyacin hali a duk lokacin da ya yi yunkurin rage yawan kudadden da ake jujuya su a cikin tattalin arzikin kasar, dabarar da akan yi amfani da ita domin rage matsala ta hauhawan farashin kayayyaki.

Karin Bayani: Babban bankin Najeriya ya dauki mataki kan bankuna

A bisa tsari idan kudin sun shiga banki shi ne za'a iya hana su fitowa. A shekarun baya irin wannan ya tilasta chanjin takardun kudin da ya kasa yin tasiri kamar yadda Mallam Yusha'u Aliyu masanin tattalin arziiki a Najeriyar ya bayyana.

Bullo da sabbin matakai na samar da lamba ga duk wanda ke da asusun ajiya a baki, wacce ke nuna nawa aka ajiye kuma a wane lokaci ta haifar da karuwar masu ajiye kudadde a gidajensu, musamman masu aikata cin hanci da rashawa domin kauce wa idon mikiya da zai iya hango su.

Karin Bayani: Tinubu ya kafa dambar yaki da cin hanci

Birnin Lagos a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

An dai sha kama mutanen da ke ajiye makudan kudadde a gidajensu, kama daga shadda zuwa tankin ruwa, ko a binne a kasa. Sai dai Dr Musa Adamu Aliyu shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ya ce suna daukar matakai don dakile cin hancin

A bayyane ta ke a fili halin da tattalin arzikin Najeriyar ke ciki wanda ya haifar da mumunan hali a kasar musamman hauhawan farashin kayayyaki da ba'a taba ganin irinsa ba, duk kuwa da yawan kudadden da ke hannun jama'a yanayin da ya bar jama'ar a hali na ga koshin ga kwannan yunwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani