APC ko ADC- Wa zai yi zawarcin Kwankwaso?
October 22, 2025
Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, zai iya hadewa da Atiku Abubakar a ADC ko Tinubu a APC amma dole akwai sharudda da ka'idoji. Kwankwaso wanda ake ci gaba da gabatar da bukukuwan murnar cikarsa shekaru 69 a duniya ya bayyana cewa, akwai alakar mutumtawa tsakaninsa da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Kwankwaso da ya kasance jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriyar, ya bayyana jin dadi bisa yadda Tinubun ya aiko masa da sakon taya murna har ma a cikin sakon ya jadadda tsohuwar alakarsu da kuma yadda suke da fahimtar juna.
Ko Kwankwaso zai shiga APC?
Amma fa wannan alaka ba tana nufin ya shiga jam'iyyarsa ba tare da sanin makomarsa da ta al'ummarsa ba, dan haka duk tafiyar da ta zo masa da tsari mai kyau na cikakkiyar makoma ga al'umma da magoya baya da shi kansa a shirye yake ya rungume ta a haye tudun mun tsira.
Kwankwaso ya bayyana cewar babban abin da ke dagula masa zuciya a siyasar wannan lokaci shi ne cin amana, domin yaga darussa da dama na yadda mutane ke bijirewa gaskiya su rufe idanu wajen cin amanar wadanda suka cicciba su.
Alaka da gwamnatin Kano
Dangane da alakarsa da gwamnatin Kano wacce ya kafa kuma Kwankwasoya bayyana cewa, tafiyarsu tafiya ce ta yin biyayya ga tsarin Kwankwasiyyya da ke nufin inganta rayuwar alumma. A cewarsa dole ana tafiya ana bayar da shawarwari, domin tafiya ce ta amana.
Kwankwaso ya yi godiya, ga dubban mutanen da suka aiko masa da sakonnin taya murna a wannan lokaci. Wani abu da har yanzu ya shigewa mutane duhu dangane da matsayar madugun na Kwankwasiyya shi ne, rashin tabbas na ci gaba da zama a cikin jam'iyyar NNPP ko kuma ficewa da komawa jam'iyyar APC ko ADC ko kuma hadewa da Goodluck Jonathan su yi takara a jam'iyyar PDP.