Ina makomar siyasar ma'aikatan Najeriya?
August 20, 2025
Wata sanarwar gwamnatin Tarayyar Najeriyar dai ta ce, ya zama wajibi ga ma'aikatan su zama 'yan kallo a fagen siyasar kasar. To sai dai kuma kungiyar kodago ta NLC ta ce, tana da daurin gindin doka wajen taka rawa cikin fagen na siyasa. Ya zuwa yanzun dai tai nasarar kafa jam'iyyar Labour da tushenta ke zaman jam'iyyyar ma'aikatan Najeriyar, kuma take taka rawa ta adawa cikin fagen na siyasa. To sai dai kuma gwamnatin kasar ta umarci masu yi mata aikin da su koma kallo, a cikin fagen mai tasiri.
Karin Bayani: Rikicin jam'iyyar Labour ya dauki wani salo a Najeriya
Wata sanarwar shugaban ma'aikatan kasar dai ta ce, dole ne ma'aikata su tsaya a matsayin 'yan da nufin tabbatar d arantsuwar adalcin da ke cikin tsarin aikin. Sanarwar kuma da ga dukkan alamu, ta bata ran kungiyar NLC ta masu kodagon Tarayyar Najeriyar. NLC dai ta ce ba halin kokarin tauye mata hakkin da ta ce, kundin tsarin mulki na kasar ya ba ta a cikin fagen na siyasa.
Kokari na gyara ga kasa ko kuma neman yin na gaban kai, ya zuwa yanzun dai ma'aikata a Najeriyar na taka rawar da ke da tasirin gaske wajen kai wa ya zuwa zabe na shugabanni a kasar. Kuma duk da cewar dai Abujar ta fake da batun adalci cikin batun yin aikin, taka rawar ma'aikatan cikin fagen na siyasa na iya tasiri ga makomar 'yan mulki a tarayyar da kila ma a jihohi.
Karin Bayani: Fargabar dorewar dimukuradiyya a Najeriya
Da kyar da gumin goshi dai Abujar tai nasarar danne jam'iyyar Labour, a zabukan tarayyar a shekaru biyu baya. Kuma a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Najeriyar, sake ragamar siyasar a banagren ma'aikatan na iya tasiri cikin fagen siyasar anan gaba. Ya zuwa yanzun da akwai alamun raba gari a tsakanin masu kodagon da ke ji a jiki, sakamakon manufofi na gwamnatin da kuma Abujar da ke fafutukar inganta aikin a cikin ikirarin rashin kudi.