Fatali da tsarin karba-karba a Najeriya
May 14, 2025
Duk da cewa tsarin na karba-karba ba ya a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma tun 1999 ake amfani da shi a kasar. An dai tabka muhawara mai zafi a tsakanin 'yan majalisar wakilan Najeriya a kan wannan kuduri, wanda tun farko mataimakin shugaban majalisar wakilan Benjamin Kalu ya gabatar da shi. A karatu na biyu ne 'yan majalisar suka yi fatali da kudurin kan dalilai mabambanta musamman cewa zai hana sakewa wajen zabe da haddasa kabilanci da wariya, kuma shiyoyi shida da ake magana a kansu ba sa cikin tsarin mulkin Najeriyar. Duk da cewa wannan tsari na karba-karba jam'iyyar PDP ce ta fara assasa shi a cikin Najeriyar, amma yana kara amo ba kawai a matakin dan takarar shugaban Najeriya ba har ma da na gwamnoni zuwa 'yan majalisun dokoki da ma shugabancin jam'iyyun siyasar kasar musamman manya daga cikinsu.#b#
#b#Mafi yawan 'yan majalisar da suka dage a kan kudurin dai sun bayyana bukatar samun daidaito ga kabilun da ba su da rinjaye a Najeriyar domin a hangensu in ba ta tsarin na karba-karba ba, ba za su taba jin kamshin kai wa ga madafan iko ko da ta hanyar zabe ne ba musamman mukamin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma na gwamnoni a jihohi. To sai dai duk da dagewarsu kudurin bai kai labari ba, a lokacin da aka kai ga kada kuri'a ta fatar baki. Fatali da wannan kudurin doka ya shafi sauran kudurin guda shida da ya kamata a yi musu karatu na biyu, wadanda suka hada da kudurin doka da ya nemi karbe ikon yi wa jam'iyyun siyasa rijista da kudurin neman dokar da za ta bayar da damar kafa ofsihin mai binciken kudi a jihohin Najeriyar.