1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zaben Najeriya soke kanan jam'iyyu

February 6, 2020

Hukumar zaben Najeriya ta fidda sanarwar cewa ta soke jam'iyyu kimanin 74 daga cikin jam'iyyu 92 da ake da su a kasar.

Nigeria Wahl 2015 Straßenszene
Hoto: Plaucheur/AFP/Getty Images

A jawabin da shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya gabatar, ya bayyana cewa jam'iyyu 18 kacal suka samu tsira a yankan almakashin da INEC ta yi. Dalilin soke rijistar jam'iyyun dai, shi ne rashin tabuka wani abu a zaben bara, abin da kuma ya kai ga soke rijistarsu daga hukumar.

Farfesa Yakubu ya kuma fada wa manema labarai cewa, hukumar zaben ta tsara ranar 10 ga watan Satumban bana a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, sai kuma 10 ga watan Oktoba inda za'a yi zaben jihar Ondo.