Najeriya: Inganta rayuwar mutanen da rikici ya shafa
February 14, 2024Sabon Shirin na da babban burin kai kauce wa karfi da mai da kai zuwa ga kwakwalwa a cikin neman mafitar rikicin makiyaya da manoma a sashen arewacin kasar.
Akalla gidaje guda 1000 za'a gina a jihohin Katsina da Sokoto da Jihar Kebbi, Ko bayan Benue da Kaduna da Zamfara da jihar Niger a karkashin shirin da ke da fatan sauya tunani na kabilar Fulani.
Karin Bayani: Miyetti Allah: Mafita kan tsaro a Najeriya
Abujar dai na kallon sabuwar dabarar da idanun mafitar rikicin na shekara da shekaru da ke zaman barazana mai girma a tsakanin al'umma.
A baya dai Abujar ta fuskanci adawa da wani shiri na samar da ruga ta zamani ga masu sana'ar kiwon da wasu ke yi wa kallon sana'ar da ke zaman ta masu neman riba.
Kuma ko yanzun daga dukkan alamu dabarar ta Pulako na shirin fuskantar adawa har cikin shugabannin kabilar ta Fulanin tarrayar Najeriya a halin yanzu.
Dr Abubakar Umar Gire jigo a kungiyar Fulani ta kasar ya ce sabon shirin bai wuci kokarin sace zuciyar fulin Najeriyar ba.
Karin Bayani: Plateau: Magance rikicin manoma da makiyaya
Babu dai kasafin da ake shirin kashewa domin aikin da ake yi wa kallon an kusa makara a kasar da ke fuskantar karuwar rikici a tsakanin makiyaya da manoma.
Sai dai kuma a fadar Nasir idris gwamnan kebbi, jihohin da ke cikin shirin a halin yanzu, na da burin kai wa har karshe a kokarin samun zaman lafiya tsakanin makiyayan da kuma manoma.
Tarrayar Najeriyar dai na asarar adadin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 14 a shekara daga rikicin makiyaya da manoman da ke kan gaba a kasar a halin yanzu.