'Yan Biafra sun fasa kauracewa zabe
February 15, 2019Talla
Babu tabbacin da wadanda kungiyar ta cimma yarjejeniyar, amma ana danganta matakin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP. 'Yan Biafra dai sun dade suna da burin samun kasa mai cikakken 'yanci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar, wannan ya sa suka umurci magoya bayansu da su kauracewa zaben 2019.
Kungiyar na son amfani da wannan lokaci domin gudanar da zabukan raba gardama, da nufin kafa kasar Biafra, sai dai shugaban kungiyar Nnamdi Kanu ya bar Najeriya tun bayan da sojoji suka kai samame gidansa a watan Satumbar shekara ta 2017.