Jami'an tsaron Najeriya na sayar da makamai
May 30, 2025
Kakakin rundunar sojojin Ademola Owolana ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, rundunar ta kaddamar da samamen ne cikin watan Agustan bara bayan da korafin satar makaman jami'an tsaro ya yawaita. A cewarsa kawo yanzu sun cafke jami'an sojoji 18 da na 'yan sandan kwantar da tarzoma 15 da fararen hula takwas ciki har da wani mai rike da sarautar gargajiya da ake zargin suna sayar da makaman ga 'yan bindiga har ma da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi. . Sama da shekaru 15 ke nan dai, Najeriyar na yaki da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso gabashi bayan ga rikicin manoma da makiyaya a Arewa maso Tsakiya da kuma 'yan aware a Kudu maso Gabashi kari da masu satar mutane domin neman kudin fansa a yankin Arewa maso Yammacin kasar.