1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ta rincabe a wasu sassan Najeriya

Abdourahamane Hassane
August 1, 2024

'Yan sandan a Najeriya sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da suka taru a babban birnin tarayya Abuja da Kano don nuna adawa da rashin shugabanci na gari da tsadar rayuwa.

Masu zanga-zanga a Abuja a shekarun bayaHoto: Reuters/A. Sotunde

 A Kano da ke arewacin kasar, masu zanga-zangar sun yi kokarin kunna wuta a kofar ofishin gwamnan, inda ‘yan sanda suka mayar da martani ta hanyar amfani da hayaki mai sa kwalla. A  Abuja ma babban birnin kasar jami'an tsaro sun tarwatsa masu gangamin.

Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, na cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki shekaru da dama, biyo bayan sauye-sauyen da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, wanda ya hau mulki a watan Mayun shekara ta 2023. Masu zanga-zangar na yin kira ga shugaba  Tinubuda ya sauya wasu gyare-gyaren da ya yi, kamar dakatar da tallafin man fetur, kana ya kawo karshen wahala da  yunwa a kasar.