1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta gaza nasara a kotu a Najeriya

August 11, 2020

A wani abun da ke zaman sabon rudani a cikin fagen siyasar Najeriya, wata kotun daukaka kara a Abuja ta nemi hukumar zaben kasar ta INEC da ta sake mai da rijistar wasu jam'iyyu 22 da ta sokewa rijista.

Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zan kanta INEC, Farfesa Mahmood YakubuHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

A cikin watan Fabarairun wannan shekarar ne dai hukumar zaben Najeriyar ta INEC ta soke jerin wasu jam'iyyu 74  bayan abun da ta kira gaza cimma ka'idar samun akalla kaso 25 cikin 100 na yawan kuri'u, a zabukan kasar da ya gabata. Abin kuma da ya bar kasar da jam'iyyu 18 kacal a cikin tsarin da masu sharhi ke masa kallon alamun tsafta cikin fagen siyasar kasar mai datti.

To sai dai tun ba'a kai ga ko'ina ba, wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja babban birnin kasar, ta nemi hukumar da ta sake mai da rijistar kimanin 22 a cikinsu, bayan da suka shigar da kara a gaban kotun suka kuma ce matakin na hukumar zaben ya saba da ka'ida.
Kotun karkashin inuwar babbar alkali mai shari'a Monica Dongban dai, ta ce INEC din ba ta cika ka'idar sashe na 225 na kundin tsarin mulkin kasar ba, wajen yanke hukuncin da ya nemi mayar da jam'iyyun  zuwa kwandon shara.

Hukumar zabe mai zaman kanta?Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Ko INEC na zaman kanta?

Sabon hukuncin  dai ya saba da wani irinsa da kotun ta fitar a karshen watan Yulin da ya gabata da a cikinsa alkalan kotun suka tabbatar da 'yancin hukumar zaben na soke rijistar jam'iyyun. Ya zuwa yanzun dai baki biyun alkalan kotun yana shirin yamutsa lamura a cikin fagen siyasar kasar da ke shirin yin sabon zabe a jihohin Edo da Ondo. Tuni dai hukumar ta INEC ta fitar da sunayen masu takarar gwamnoni a jihohin guda biyu, ba tare da la'akari da dama ta ragowar jam'iyyun 22 da suka daukaka karar ba.

Nick Dazang dai na zaman kakakin hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriyar wato INEC, kuma ya ce  hukumar ba ta da zabi face tafiya kotun koli da nufin tantance aya cikin tsakuwa na hukuncin da ya daure cikin hukumar zaben.

Harabar kotun kolin NajeriyaHoto: U.A. Idris

Ko wanne irin tasiri hukuncin kotun ka iya yi ga zabukan guda biyu da ke dada daukar zafi da hankalin al'ummar Najeriyar, babban zargi da mafi yawan jam'iyyun ke fuskanta na zaman mai da kansu zuwa jam'iyyun babba da jaka, maimakon goga kafada cikin fage na siyasar domin samun kuri'a ta 'yan kasa.

Jam'iyyu 'yan amshin shata

Ko bayan karewa ba nasara ta kama ko da dan bera a cikin farauta, ana kuma zargin da yawa a cikin jam'iyyun da zama 'yan amshin shatar manyan jam'iyyun kasar da kuma sukan kare tare da halasta haramcin da ake zargi yayin zabukan. Inusa Tanko dai na zaman shugaban jam'iyyar National Concience Party, guda cikin jam'iyyun da suka fuskanci gatarin na hukumar zaben da kuma ya ce babu gaskiya a cikin jerin zargin da ke kama da kokari na rataye kare bisa laifin kura a fagen na siyasa. Har ya zuwa yanzu dai Najeriyar na fuskantar jerin matsala a kokarin gyara tsarin zaben da ke iya gina imani na daukacin 'yan kasar bisa abun da ke faruwa a dandalin siyasar da ke neman koma wa iya karfinka iya shagalin ka.