Najeriya: Kalubalen da ke a gaban Super Eagles
November 26, 2018A Najeriya duk da nasarar samun kaiwa ga cancatar da kungiyar kwallon kafan Super Eagles ta Najeriya ta yi ta zama jerin kasashen da za su hallartar gasar cin kofin kasashen Afrika na Afcon da za’a yi a badi, da alamun akwai sauran aiki a gaban kungiyar ta la'akari da wasu matsaloli na salon wasa da kungiyar ta nuna a wasan sada zumunta da ta yi da Uganda.
A wasannin bundesligar kasar Jamus kuma kungiyar Dortmund na ci gaba da jan zarenta a saman tebirin Bundesliga da maki 30 a yayin da Yaya Babba Bayern Münich ke ci gaba da fuskantar koma baya, inda a yanzu take a matsayin ta biyar da maki 21 bayan da ta tashi ci uku da uku a karawar da ta yi a gida a karshen mako da kungiyar Düsseldorf.
A gasar zari ruga Faransa da ke daya daga cikin jiga-jigan kasashe a wasan ta kwashi kashinta a hannun kasar Fji, lokacin fafatawa a karshen mako, inda Fiji ta doke Faransa 21 da 14.Wannan na wakana ne a daidai lokacin day a rage kasa da shekara guda kafin gasar cin kofin zari ruga na duniya a shekara mai zuwa da japan za ta dauki nauyi, inda Faransa take rukunin na uku na C, tare da kasashen Argentina, Amirka da Tonga da kuma Ingila.