1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya takardun Naira ya janyo kalubale

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 16, 2023

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da izinin amfani da tsohuwar Naira 200 saboda matsalolin da ya haifar, abin tambaya shi ne mai ya janyo kalubalen ganin ba yanzu aka fara sauya kudin kasar ba?

Najeriya | Bankuna | Naira | Zabe | 2023
Ba dai a layin mai ne kawwai ake dogon layi a Najeriya ba, har ma da bankunaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Tun dai a shekara ta 1965 ake canja takardun kudin na Naira, sauya fasalin takardun kudin da doka ta bai wa babban bankin kasar damar yi bayan shekaru biyar zuwa takwas. Duk da cewa sauya fasalin kudin ko kuwa canjin kudin babban al'amari ne a Najeriya domin yana tilasta fito da tsohuwar ajiya, amma a lokutan baya an yi hakan cikin sauki ba tare da fusknatar kalubalen da ake gani a yanzu ba. Daukar salon shari'a da ma biris da hukuncin kotun koli da gwamnan babban bankin Najeriyar ya yi a kan batun chanjin kudi, har yanzu na haifar da rudani. Duk da amfani na manufofin da ke tattare da sauyin fasalin kudin da gwamnatin Najeriyar ta bayyana a daidai lokacin da kasar ke tunkarar zabe, lamari ne da alummar kasar ba za su mance da shi ba. Sauya kudin dai ya jefa al'ummar cikin yanayi na kai da kudinka a hana ka taba su, abin da ya haifar da ga koshi ga kwanan yunwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani