1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kamfanoni na rufewa saboda tsadar mai

September 28, 2023

A wani abun da ke zaman sabuwar barazana ga tattalin arzikin Najeirya, kamfanonin kasar na rufewa sakamakon tashin farashin man diesel da kuma hauhawan farashin da ke karuwa a kasar

Wata 'yar kasuwa a Lagos Najeriya
Wata 'yar kasuwa a Lagos NajeriyaHoto: P. U. Ekpei/AFP/Getty Images

Kungiyar masu masana'antu a  Najeriyata ce akalla kamfanoni 95 ne a kasar ke rufewa a shekara sakamakon hauhawan farashin makamashi da ma kudin Dala bayan talauci da ke karuwa a kasar a halin yanzu

Wani rahoton kungiyar masana'antun ya ce a farkon watanni Shida na shekarar bana (2023) an yi asarar ayyuka sama da 3,500 sakamakon kulle shaguna a bangren masana'antun da ke ta ji ba dadi.

Dan kasuwar chanjin kudi a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Dalar Amurka guda dai na shirin kaiwa Naira 1000 na Najeriya ko bayan man na diesel da masana'antun da suka dogara da shi da ya kai Naira 1100 kowace lita.

Karin Bayani: Najeriya: Fata kan matatar man Dangote

Hajiya Husaina Ahmed Umar dai na zaman shugabar kamfanin Amalco da ke sarrafa man gyada a Kano, kuma ta ce abubuwa sun yi baki cikin masana'antun yanzu.

Kayyayakin da suka kai Naira miliyan dubu 270 ne dai ke ajiye a kamfanonin babu masu saye, sakamakon tsadar rayuwar da ta tilasta mayar da hankali ga abinci maimakon bukatun jin dadi a kasar.

Hada-hadar kasuwanci a jihar Lagos a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Tuni dai dama gwamnatin kasar ta zare tallafi bisa man na Deisel da ke zaman mafi tasiri ga rayuwa cikin kasar a halin yanzu.

Ibrahim Shehu Yahaya na zaman sakataren dillallan mai a Najeriya wanda ya ce tashin farashin dala na zama na kan gaba bisa tsadar makamashin abun alfahari na kamfanonin kasar.

Dada nisa cikin masifa ga kasa, sannu a hankali dai jari hujjar da ta kai mahukuntan kasar ga zare tallafi a rayuwa da makoma na neman bada ruwa a kasar.

Gwajin dabaru iri-iri na kara jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani ga Najeiryar da ke tunanin girma amma kuma ke dada kallon karuwar talauci.

Babban burin mahukunta na saita tattalin arzikin Najeriyar da nufin takara a kasuwar kasashen Africa dai na neman komawa ya zuwa mafarkin rana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani