1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin harajin hada-hadar kudi da bankuna a Najeriya

September 18, 2019

Babban Bankin Najeriya ya fitar da wata sanarwa da take dauke da karin haraji ga duk wadanda suke mu'amala da fitar da kudi ko shigarwa a bankunan kasar.

Zentralbank von Nigeria

Bankin na CBN ya ce ya dauki wannan tsari ne don tabbatar da abin da ya kira rage amfani da tsabar kudi wato Cashless Policy a Turance wato mu'amala da kudade ba sai an debo su a buhunhuna ba a kasar, domin yin haka na haifar da barazana ta fannin tsaro.

A wata sanarwa da ta fito daga bankin a wannan Laraba dauke da sanya hannun daraktan harkokin yau da kullum Mr Sam Okoreje ta ce daga yanzu duk wanda zai fitar da kudi a na'urar cire kudi wato ATM zai ba da haraji na kaso 3 cikin 100 na adadin kudin da ya fitar ko kuma ya shigar za a karbi kaso 2 cikin 100, musamman ga kudaden da suka haura Naira dubu 500.

A dangane da kamfanoni kuwa duk kamfanin da ya fitar da kudi sama da miliyan ukku zai ba da kaso 5 cikin 100.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannan tsarin kuwa zai fara aiki ne daga wannan Laraba a jihohin Legas, Kano, Anambra, Ogun, Abia da kuma Rivers.

Masu hulda da bankuna sun bayyana ra'ayoyinsu suna masu cewa ba abu ne mai kyau ba illa dai wata hanya ce ta kassara talakawan gari. Wasu kuma sun kwatanta matakin da cewa wata kafa ce ta cin zarafin dan Adam inda suka yi kira ga hukuma ta sake tunani.

Dr Nkiruka Maude masaniya ce ta fannin tattalin arzikin kasa a Najeriya da ta ce wannan tsarin na tafe ne da yadda kudade ke shiga a kowacce rana, amma fitar da kudi ko shigarwa musamman ga kamfanoni da kaso 5r cikin 100 babu shakka batu ne da hankali ma ba zai karba ba sai ka ce 'yan Najeria ba sa biyan haraji ga sauran sassan rayuwa na kasar.

A ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2020 duka jihohin Najeriya za su dauki tsarin baki daya don cimma manufar da aka sanya a gaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani