Najeriya: Fargaban al'umma a kan sha'anin tsaro
May 11, 2018To wannan kiraye kiraye da shugabannin kungiyar ta Miyetti Allah suka yi dai ya biyo bayan irin kamen da jami'an tsaron suka yi ne a tsakanin makon jiya da kuma wannan mako. Inda ko da a ranar Talata da ta gabata ma dai rundunar sojin Najeriya ta gabatar wa manema labarai wasu 'yan bindiga da ta ce ta kamo su da manyan makamai a kauyen Tsedum da ke cikin karamar hukumar Guma ta Jihar Benue. Ita ma rundunar 'yan sanda ta gabatar wa manema labarai wasu da take zargi da kai hare-hare kan al'ummomi da ke tsakanin Jihohin Benue Nasarawa da Taraba, cikin su akwai wani da ake kira Morris Ashwe, dan hasalin yankin Mbajimba da ke karamar hukumar Katsina Alla cikin jihar Benue. wanda ya amsa cewar shi ne ke samar da makamai ga fittacen dan bindigar nan Tarwase Akwaza da jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo.