1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kasa mafi yawan yara da ba sa makaranta

Abdullahi Tanko Bala
November 19, 2024

Duk da karuwar miliyoyin yaran da basu sami damar karatu ba, jihohin tarayyar Najeriya na nuna ko in kula da harkokin ilimi a matakan farko na kasar.

Nigeria Freilassung entführter Schülerinnen
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Ya zuwa yanzu tarayyar Najeriyar ta zarta Indiya ta kuma ciri tutar zama kan gaba wajen yaran da basu da damar karatu. Kididdigar hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara miliyan 18 na gararamba a gari sakamako rashin zuwa makaranta da ke ta karuwa cikin kasar a halin yanzu.

Sai dai kuma akalla wasu Naira miliyan dubu 135 na kudaden tallafa wa ilimin makarantun firamare da sakandare ne ke bankuna suna shan kura sakamakon gazawar jihohin kasar na nuna bukata.

Karin Bayani:Dalibai sun samu izinin ciyo bashin kudin makaranta a Najeriya 

Wasu yara yan makarantar firamare a jihar Lagos, NajeriyaHoto: DW

Jihohi 34 cikin 36 da ke tarayyar Najeriyar dai sun kau da kai bisa dukiyar da ke karkashin hukumar kula da IIlmi a matakin farko ta kasar, da kuma ke da babban burin kyautata ilimi a kasar.

Ibrahim Jibo tsohon kwamishinan tsara tattalin arziki a Zamfara da kuma yace cin hanci na kan gaba cikin hujjar ko in kula kan makomar miliyoyin yaran kasar.

Karin Bayani:Najeriya za ta kafa rundunar tsaro don kare makarantu

Wasu yara dalibai yan makaranta a NajeriyaHoto: Benson Ibeabuchi/AFP/Getty Images

Koma ya take shirin kayawa a tsakanin turawan da ke gadin dukiya da masu siyasar da ke tunanin dama, a mafi yawan jihohin Najeriyar, jari a cikin harkar ilimin na nufin ginin karin azuzuwan karatu amma kuma babbar dama ta kwangila ga masu mulki a jihohin.

Farfesa Kabir Bello kwarrare a harkar ilimin, ya ce daidaito cikin batun karatun bai kare cikin ginin aji a makarantu ba.

Karin Bayani: Makomar karatun miliyoyin yara a Afirka

Yara yan mata yan makaranta a Kano NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Jihohin arewa maso yammacin kasar da ke da yara kusan miliyan takwas da basa makaranta na zama baya ga dangi wajen batun iya karbar kudaden.

Katsina dai na da Naira miliyan dubu 1.39 da ta kasa karba, haka kuma adadin yake a jihohin Kaduna da Kebbi.

Kano ma na da kusan Naira miliyan 581 da ke a hannun hukumar kula da harkokin ilimin na matakin farko.