1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin badi sai da bashi a Najeriya

August 30, 2022

Alamun sauyi ga tattalin arziki da zamantakewar Tarayyar Najeriya a shekarar badi, inda gwamnati ta ce da kamar wuya ta iya gudanar da manyan ayyuka sakamakon rashin kudin da ke neman tilasta mata cin babban bashi.

Najeriya | Bashi | Naira | Tsadar Rayuwa
Bashi na neman zamarwa Najeriya mutu ka raba takamin kazaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da cewar dai ana karatun tsadar mai d kila ma karuwar kudin shiga a cikin aljihun gwamnatoci a kasar, shekarar da ke shirin zuwa dai na zaman mai wahala a idanun 'yan mulkin Tarayyar Najeriyar. Kuma tun ba a kai ko'ina ba dai, Abujar ta ce tana shirin cin bashin da ya haura Naira triliyan 11 kafin iya aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar badi. Kasafin da ke zaman irinsa na karshe ga masu tsintsiyar da ke fatan dorawa kan mulki dai, a fadar ma'aikatar kudin kasar na iya karewa ba tare da samar da kudin aiwatar da manyan aiyyukan da Abujar ke fatan kammaluwarsu ba.

Karin Bayani: Tsadar rayuwa da karin kudin ruwa a Najeriya

Kama daga hanyar da ta hada Abuja da Kano a sashen arewacin kasar ya zuwa 'yar uwarta ta Ibadan ya zuwa birnin Ikko, ko bayan sabuwar gadar Niger da ke yankin Kudu maso Gabas dai, masu tsintsiyar na takama da manyan ayyukan da suke fatan su kamalla kafin kare mulkin. To sai dai kuma daga dukkan alamu daukacin kasafin kudin na Naira Triliyan 19 dai, zai kare ne a tsakanin samar da tallafin man fetur ya zuwa albashin ma'aikata da ragowar bukatun rayuwar yau da ta gobe. Dakta Isa Abdullahi dai na zaman mai sharhi kan tattalin arzikin Najeriyar da kuma ya ce, kasafin ya saba da tsarin tattalin arziki irin na manyan kasashen duniya.

Duk da kasancewarta cikin kasashe masu arzikin man fetur, al'umma na cikin halin taskuHoto: dpa

Babban fatan 'yan mulkin Najeriyar dai na zaman kai karshen al'adar shigar da mai cikin kasar da kila bayar da tallafin da ke shirin karewa daga tsakiyar shekara, a lokacin da ake fatan kammala gyaran manyan matatun man kasar guda hudu da kila ma fara aiki a matatar Dangote. To sai dai kuma a fadar Mele Kyari da ke zaman shugaban kamfanin mai na kasar da kyar da kamar wuya, a samu sauyin da ake fata daga tallafin da ke shirin lashe sama da Naira tiriliyan uku a farkon watanni shidan badin. Takai takai karatun kura dai, ana saka ran iya aiwatar da daukacin kasafin ne ya zuwa watanni shida na farko na shekarar, a yayin kuma da Abujar ke shirin mika mulki zuwa ga sabuwar gwamnatin da ke shirin hawa gado.

Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai

Sanata Umar Tsauri dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar PDP ta adawa da kuma ke fatan su kwace goruba a hannun kuturu, kuma a cewarsa dan takararsu ba ya tsoron bashin da ka iya zama gado ga gwamnatin da suke fatan su kafa. Abun jira a gani dai na zaman hanyar fitar da wando ta tsakar kai a Najeriyar da sannu a hankali ke dada fadawa cikin rikicin rashin kudi, kuma ke kallon bashi ne hanyar warware matsala maimakon tsuke bakin aljihun 'yan mulki na kasar. Kuma ya zuwa watan Maris din da ya shude dai Tarayyar Najeriyar na da basukan da suka kai dalar Amirka miliyan dubu 100 a wuyanta.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani