Najeriya: Kayayyaki na kara tsada
February 16, 2024![Hada-hada a birnin Lagos na Najeriya](https://static.dw.com/image/63766264_800.webp)
Wata sabuwar kiddidiga a tarryar Najeriyar ta ce kasar na fuskantar hauhawar farashin abinci da makamashi da kaso daya cikin dari tsakanin watan Disamba na 2023 zuwa watan Janairu 2024
Hukumar ta ce hauhawar ta karu da kaso 28.9 cikin watan Disamban bara ya zuwa kaso 29.9 a Janairun bana, adadin da ke zaman mafi girma cikin kasar a shekara da shekaru.
Tun a wata Satumban da ya shude ne dai Abujar ta ayyana dokar ta baci kan batun Abinci, sai dai kuma sai a cikin makon da ya gabata ne hukumomin kasar suka sanar da wani shirin samar da ton 42,000 na abincin.
Karin Bayani: Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya
Shi kansa babban bankin kasar CBN na kokawar inganta dalar da yace tana kara yawa cikin kasar a halin yanzu, amma kuma al'umma na kallon rushewar kasuwannin canjin
Akalla dalar Amurka kusan miliyan dubu biyu ne bankin ya ce sun shigo kasar cikin makon da ya shude, amma kuma suka gaza tasirin da yan kasar ke fatan gani.
Ya zuwa wannan ranar dai dalar ta haura Naira 1,600 kan kowace dala, adadi mafi rushewa a daukacin tarihinta.
Dr Isa Abdullahi kwarrare kan tattalin arziki ya ce ana da bambancin gaske tsakanin fada da kokarin cikawa a bangaren hukumomin wajen neman mafitar rikicin mai tasiri.
Karin Bayani: Taron neman hanyar magance matsalar abinci
Dabarbaru ko gazawar gwamnati, CBN dai ya ce yana da burin rage hauhawar zuwa kaso 21.4 kafin karshen shekarar 2024.
Duk da cewar dai tun cikin watan Oktoban da ya shude ya zamo gwamnan bankin, har ya zuwa yanzu Oluyemi Cardoso bai kira babban taron nazarin manufofin kudin kasar da ke cikin rudani ba. A fadar Yusha'u Aliyu mai sharhi kan tattalin arzikin kasar CBN din na taka rawa wajen rushewar batun kudin dama wadatar ta abinci.
Ya zuwa yanzun dai hauhawar farashin na neman rikidewa zuwa barazanar zaman lafiya a tarrayar Najeriya, kasar da tuni shugaban addinai da kabilu suke fadin ana bukatar gyara da nufin kaucewa zuciyar mai tsumma.