1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar fasahar 5G a Najeriya

August 24, 2022

Bayan share tsawo na lokaci ana tababa, Tarayyar Najeriya ta bi sahun kasashen da ke shirin cin moriyar fasahar sadarwar 5G, inda babban kamfanin sadarwar kasar MTN ya sanar da kaddamar da fasahar.

ATT | Verizon | Fasahar Sadarwa ta 5G
Tuni dai aka kaddamar da fasahar sadarwar ta 5G a kasashe da damaHoto: Andre M. Chang/ZUMA/picture alliance

A cikin watan Disambar bara ne dai, Hukumar Sadarwa ta kasar NCC, ta gabatar da sabuwar fasahar sadarwar ga kamfanonin kasar. MTN da ke zaman mafi girma a kasar da kuma sabon kamfanin MAFAB ne dai sukai nasara tare da alkawarin kaddamar da sabuwar fasahar. Koda yake MAFAB din ya nemi karin watanni biyar a hannun mahukuntan kasar, tuni MTN ya sanar da kaddamar da fasahar. Kamfanin dai ya nemi masu sha'awar fara amfani da ita su nemi wayoyi da ragowar kafafen sadarwar domin fara amfani da fasahar a biranen Abuja da Legas da ake shirin fara aiki da ita nan take.

Kamfanin ya kuma ce za a kara yawan biranen da za su ci moriyar fasahar zuwa Kano da Fatakwal da Enugu nan da wata guda. Matakin MTN din dai ya kai karshen doguwar takaddama kan alfanun fasahar da a baya aka rika yi wa kallon mai illa har ga lafiyar al'aumma, ko bayan nan dai kuma a fadar ministan sadarwa na kasar  Isa Ali Pantami fasahar na iya kawo sauyi ga tattalin arziki da rayuwar al'umma. Tarrayar Najeriyar dai na zaman kasa ta farko a yankin yammacin  Afirka kana guda cikin kasashe shida  a nahiyar da sukai nasarar kaddamar da fasahar sadarwar ta 5G.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani