1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Goodluck Jonathan a Najeriya

January 4, 2022

Batun takarar shugabancin Najeriya daga tsohon shugabanta Goodluck Ebele Jonathan ya jawo babbar muhawara a cikin kasar.

Ghana Accra| ECOWAS zur Lage in Mali | Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan ne dai babban jakadan ECOWAS da ke sasanta rikicin MaliHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

A baya dai ana yi masa take da "mai nasara" a cikin siyasar Tarayyar Najeriya, kuma ya yi nasarar tashi daga mataimakin shugaban karamar hukuma zuwa shugaban kasar cikin tsawon kasa da shekaru 20. To sai dai kuma duk da kafa tarihi na kasancewa shugaban da ya fadi a zabe tare da mika mulki ga adawa a Najeriyar, sake ambato sunansa cikin takarar shugaban kasar na shirin yamutsa hazo na siyasa. Wata ganawa tsakanin shugaban da ke kan mulki a Najeriyar da Jonathan a makon daya shude dai, ta sake tayar da kura a cikin fagen siyasar kasar. Ganawar kuma da ta kare tare da tsohon shugaban karkade makaman yaki da tayar da rundunar da yake fatan ka iya zama sojojin yakin neman mulkin na shekara ta 2023, tare kuma da ta jawo ka-ce-na-ce har a cikin jam'iyyar PDP ta adawa da ta zargi APC mai mulki da zawarcin Jonathan din domin son rai. Umar Sani na zaman kakakin tsohon mataimakin shugaban Najeriya a zamanin Jonathan din, kuma a cewarsa fitar ta shi ba zai sauya rawa cikin jam'iyyar PDP da ya ce tana shirin daukar mulki ba.

Al'ummar Najeriya, na shirin sake kada kuri'unsu a 2023Hoto: DW/Gänsler

Tuni dai Jonathan din ya kauracewa harkokin jam'iyyar PDP da ya hau bayanta wajen kai wa zuwa ga mulki na kasar, kuma babakeren gwamnonin jam'iyyar adawar Najeriyar ta PDP ya sa da kamar wuya ga tsohon shugaban cika burin ragowar shekaru hudu a kan mulkin kasar a fadar Shehu Musa Gabam da ke zaman sakataren jam'iyyar SDP na kasa. To sai dai kuma in har an raba gari a tsakanin tsohon shugaban kasar da gwamnonin PDP, an kuma dauki lokaci ana danyen ganye a tsakani na Buharin da Jonathan, abin da ake ganin ya sanya nada tshon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan a matsayin manzo na musamman a cikin rikicin siyasar kasar Mali. Takarar Jonathan din a cikin APC dai, na nufin kai karshen fatan komawar mulki zuwa Kudu maso Yammacin kasar da ke fatan dorawa daga shugabancin na Buhari. Sai dai kuma tashi daga shugaban kasar PDP ya zuwa takara ta shugaban kasar a karkashin APC, a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan al'amuran siyasar Najeriyar na zaman alamun rushewar akida a cikin fagen siyasar kasar a halin yanzu. Nasarar shugabanci na Jonathan dai, na iya sake jafa sabon fata a tsakani na masu siyasar arewacin kasar na karbar mulki nan da shekaru hudu masu zuwa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani