1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na shakku kan sahihancin zaben 2027

January 23, 2026

Kasa da shekara guda a gudanar da babban zabe a Najeriya, 'yan adawa da kungiyoyi masu sa ido kan zabe na dora aya ta tambaya bisa makomar zaben da kila ma sahihancinsa

Jagoran yan adawa a Najeriya Atiku Abubakar
Jagoran yan adawa a Najeriya Atiku Abubakar Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Har ya zuwa yanzu dai majalisar dattawan Najeriyar ta kasa amincewa da sabuwar dokar zaben a yayin da mafi yawan yan kasar ke nunin yatsa bisa iya samun sahihin zabe a bangaren hukumar zaben kasar INEC. Najeriyar dai na shirin komawa rumfunan zaben a tsakanin watan Nuwamban da ke tafe zuwa Fabrairun 2027 

Kama daga masu adawar da ke shirin taka rawa, ya zuwa yan kallo a zabukan da ke tafe hankula na dada tashi a tarayyar Najeriya bisa yiwuwar sake kwatawa a zabukan kasar na gaba. Kurakurai da daman gaske da suka hada da sanar da sakamako kai tsaye da damar zaben wuri ne dai majalisun kasar guda biyu suka nemi su gyara a sabuwar dokar zaben shekarar da ta shude.

Tsarin rumfar zabe a NajeriyaHoto: Reuters/A. Sotunde

To sai dai kuma a yayin da majalisar wakilan kasar ta amince da dokar, yan uwansu na dattawan dai sun ja kafa har ya zuwa watan Janairu na 2026 ba tare da nuna alamun amincewa da daftarin sabuwar dokar ba.

Abun da ya dauki hankali cikin kasar tare da gargadin komawa gidan jiya a bangaren tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, da ke fadin da kamar wuya sahihin zabe ya tabbata a kasar ba tare da sabuwar dokar zaben ba. Gargadin na Atiku Abubakar dai na zuwa ne a lokacin da gungun masu kallon zaben suke fadin tarayyar Najeriyar tana shirin fadawa rudu ba tare da sauyin rawa a bangaren dattawan ba.

Ana dai lissafin zaben na shekara ta 2023 a matsayin na baya ga dangi cikin batun sahihanci, bayan da hukumar zaben kasar INEC ta sa kafa ta shure tsari da matakan zaben iri-iri bisa hujjar basa tsarin doka. Ladan Salihu mataimakin kakakin jam’iyyar ADC ta Atiku ya ce rawa cikin gidan dattawan ne ke sanya tsoro a zukatan yan kasar a halin yanzu.

Tsarin rumfar zabe a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Kokarin cika buri ko kuma gyara kura-kuran baya, tuni INEC ta samu sabon shugabanci, ko bayan alkawuran inganci a cikin tsarin zabukan duk a kokarin sauya da dama a cikin suna da kila ma kimarta. 

Wata kuri’ar jin ra‘ayi da kungiyar Yiaga Africa mai kallon zabe ta gudanar, alal ga misali, na nuna mafi yawan yan kasar basu da imani na sahihin zabe a bangaren hukumar zaben. 

Nasara ko asarar zaben dai, Najeriyar tana tsakanin kai wa ya zuwa sahihin zabe, da kuma fuskantar fushin kasar Amurka da sannu a hankali ke maida ido zuwa cikin kasar a halin yanzu.

Duk da cewar dai ta iso cikin batu na kare hakki, hankalin Amurkawan dai sannu a hankali na karkata zuwa ga shugabanci na gaba cikin kasar da ke zaman mafi tasiri a nahiyar Africa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani