1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Koma bayan arziki na shafar kasuwanni

August 28, 2018

A Najeriya hannayen jari na ci gaba da fuskantar kalubale a bisa yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da samun tsaiko a fannoni da dama.

Nigeria Geldwechsler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sanya hannayen jari da sunan kasuwanci musamman a Najeriya na cigaba da tangal-tangal. inda a lokuta da dama ake samun faduwar kasuwar hada-hadar hannun jari.

Wannan ta sanya shugaban gungun kamfanin APT Ventures Alhaji Kasumu Kurfi ya yi karin haske kan halin da kasuwar ke ciki a Najeriya.

"A bisa hangen nesa na masana sun cimma daidaito cewa yadda kasuwar take haka zai haifar da yadda fannonin tattalin arzikin kasar zai nuna walau a manyan wurare ko kasuwannin marasa karfi."

Babban bankin Najeriya da ke a birnin Abuja

A yanzu haka dai ana fuskantar matsi na rayuwa bisa yadda 'yan kasuwa da kutungwila irin ta siyasa ke haifar da tsaikon ci gaba da rayuwa yadda ya kamata.

Prof. Uche Uwakele masani ne a fannin kasuwar shunku a Najeriyaa ga abin da yake cewa.

"Gaskiya ne yadda kasuwar ke tafiya shi ke shafar fannin tattalin arzikin kasa kuma muna fuskantar kalubale tun daga watan Fabrairu kawo yanzu kuma hakan ba ya rasa nasaba da fannin tattalin arzikin kasar Najeriya."

Malama Rahma Usman tana da alaka da sayen hannun jari a Najeriya ta nuna yadda take kallon batun a yanzu haka.

"Tun a kusan shekaru 10 kenan nake da alaka da sayen hannayen jari amma kuma jiya iyau babu wani abin a zo a gani."

Mr Yusuf Olayinka masani ne a fannin kasuwar shunku a Legas da ke cewa kasuwar shunku kasuwa ce ta karuwa da kasuwanci sai dai bai dace a sanya kudi baki daya ba a kasuwar, sai dai a sanya ribar da aka samu ta wani fannin inda ta haka ne kwalliya za ta biya kudin sabulu.

To sai dai a kullum gwamnati da masana na ikirarin cewa gyara ya fi daukar lokaci da yin barna a rayuwar dan Adam.