1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta soke wasu sassan dokar INEC

May 22, 2026

Kotun dai ta ce ba hujja ga hukumar zabe INEC na takaita lokaci a daukacin shirin zabukan Najeriyar da ke tafe.

Babbar kotun tarayya ta Abuja
Babbar kotun tarayya ta AbujaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Tuni dai daukacin jam'iyyu Najeriyar suka mika rijistar yayansu ga hukumar zabe INEC cikin cikon umarni, a yayin kuma da suke da zuwa karshen watan Mayun domin mika sunayen masu takara ga hukumar duk a karkashin wani jadawali da hukumar ta takaita.

Kafin kotun da ke Abuja ta sa kafa ta shure tsarin da ya toshe kafa ta sauyin sheka, cikin fagen siyasar. Kotun ta ce jam'iyyun kasar na iya mika rijistar yayansu da masu takara har ya zuwa watan Satumban da ke tafe.

Matasa magoya bayan siyasaHoto: DW

Yabo da jinjina ya mamaye jam'iyyun adawar da ke fatan cin moriya cikin rigingimun gidan APC .

Yancin rawa da watayawa cikin fagen siyasa, ko kuma mai da hannun agogo zuwa baya dai, sabon hukuncin kotun na zuwa ne a lokacin da rigingimu suke kara sama cikin fagen siyasar.

Masu adawar dai na kallon fatan da ke da girman gaske cikin rigingimun da ke a jam'iyyar APC. Rigingimun kuma da ke iya kaiwa ya zuwa sauyin sheka a bangaren masu takara da kila magoya bayansu.

'Yan siyasar NajeriyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

To sai dai kuma daga dukkan alamu masu adawar suna da babban aiki a kokarin burge masu korafi cikin gidan APC yar mulki. Mustapha Mai Haja dai ya tsaya takara ta gwamna a Jihar Yobe, kuma yace bashi da niyyar sauyin sheka zuwa cikin gidan adawa a nan gaba.

Mika gaskiya inda ta dace ko kuma neman cika burin son rai, ko bayan jam'iyyun adawa, sabon hukuncin na iya tasiri har cikin majalisar dattawa ta kasar inda kusan rabin Yayan dokar ke shririn adabo da tunanin dokar a karkashin tsohon tsarin.

Yan kwanakin da kila watannin da ke tafe dai na shirin yanke hukunci bisa rawa ta zuciyar mai tsumman a kokarin neman damar takara cikin fagen siyasar kasar.