Najeriya: Kotu ta yi watsi da karan 'yan Shi'a
July 7, 2017![Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye](https://static.dw.com/image/18889826_800.webp)
Talla
Jagiran 'yan Shi'a Ibrahim Zakzaky ya nemi a biya shi diya ta Naira bliyan biyu bayan arangamar da aka sha tsakanin 'yan Shi'ar da sojojin Najeriyar. A cikin watan Disamba na shekara ta 2015 a garin Zariya da ke cikin jihar Kaduna a yanki arewa maso gabashin kasar wanda a ciki mutane 350 suka mutu.